
Dehqan: Babu Batun Tattaunawa Tsakanin Iran Da Amurka
Tuesday, 23 June 2020
Comment
Babban mai baiwa jagoran juyin juya halin muslunci a Iran shawara kan harkokin soji Birgediya Janar Hussain Dehqan ya bayyana cewa, babu batun tattaunawa tsakanin Amurka da Iran.
A zantawarsa da tashar Aljazeera wadda a aka watsa a jiya, tsohon ministan tsaron kasar Iran, kuma babban mai baiwa jagoran juyin juya halin muslunci a Iran shawara kan harkokin soji Birgediya Janar Hussain Dehqan, ya jaddada cewa, babu wani batu na tattaunawa tsakanisnu da Amurka.
Ya ce, ba su kallon Donald Trump a matsayin shugaban kasa, suna kallonsa a matsayin wani mutum maras kan gado, wanda ya aikata manyan laifuka ga al’ummar Iran da ma al’ummomin duniya, saboda haka babu batun tattaunawa da shi.
Dangane da alaka tsakanin Iran da UAE kuwa, Janar Dehqan ya bayyana cewa, a cikin lokutan baya-bayan nan alaka tana kyautata tsakanin kasashen biyu.
A lokacin da yake amsa tambaya kan dangantakar Iran da Saudiyya kuwa, Dehqan ya ce Iran ba ta da wata matsalar tattaunawa da Saudiyya a duk lokacin da gwamnatin ta Saudiyya take bukatar hakan.
Dangane da rikin Libya kuwa ya bayyana cewa, samun hadin kai da yin sulhu tsakanin dukaknin bangarorin siyasa a kasar Libya, shi ne kadai abin da zai kawo karshen rikicin kasar.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Dehqan: Babu Batun Tattaunawa Tsakanin Iran Da Amurka"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?