Da yiwuwar za a dawo da zirga-zirga tsakanin jihohi a ranar 21 ga watan Yuni - Sani Aliyu
Thursday, 4 June 2020
Comment
ROHOTON: LEGIT.NG
Akwai alamu da ke nuna cewa da yiwuwar za a cire dokar hana zirga-zirga tsakanin jihohi a ranar Lahadi, 21 ga watan Yuni. Babban jami'i a kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da cutar korona, Sani Aliyu, shi ne ya ambato hakan cikin wata sanarwa da ya gabatar a ranar Talata, 2 ga watan Yuni. Aliyu ya lura cewa,
muddin aka dawo da tashin jiragen sama cikin gida, to ba zai dace ba a ci gaba da dokar hana zirga-zirga tsakanin jihohi. Tun a watan Maris ne Gwamnatin Tarayya ta shimfida dokar hana zirga-zirga tsakanin jihohi a fafutukar da ta ke yi na dakile yaduwar cutar korona a fadin kasar.
Sai dai ana zargin jami'an tsaro sun taya al'umma sabawa wannan doka, yayin da suka rika bai wa matafiya damar yin shige-da-fice tsakanin jihohi bayan karbar na goro.
Da ya ke jawabi a zaman karin haske karo na 39 kan halin da kasar ta ke cikin game da annobar korona a ranar Talata, Aliyu ya ce har yanzu dokar hana zirga-zirga tsakanin jihohi tana nan daram.
Sai dai ya ce dokar za ta yi afuwa ga masu safarar kayan abinci da amfanin gona, makamashin mai, da kuma sauran muhimman kayayyakin bukata da makamantansu. Da yake karin haske kan lamari, ya ce ana sa ran za a dawo da jigilar jirgin saman cikin gida a ranar 21 ga watan Yuni. Yace "babu lallai hakan ya tabbata a wannan rana, domin kuwa yana iya kasancewa, ranar 26, ko 28, ko kuma ma 1 ga watan Yuli."
"Ya danganta da irin shirin da ma'aikatar sufurin jiragen saman ta yi. Mun dai kayyade musu lokaci na makonni uku su fara shirye-shiryen dawo da jigilar jiragen saman cikin gida." Bayan da gwamnatin Tarayya ta sassauta dokar kulle tare da ba da umarnin dawo da jigilar jiragen saman cikin gida, ta fidda sunayen filayen jiragen sama biyar da za a bude a kasar.
Kaftin Musa Nuhu, shugaban hukumar sufurin jiragen sama (NCAA), shi ne ya sanar da hakan a wata wasika mai kwanan watan 1 ga Yunin 2020. Kamar yadda NCAA ta bayyana, filayen jiragen saman da za a bude su ne:
1. Filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Legas.
2. Filin jirgin Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
3. Filin tashi da saukar jiragen saman da ke Fatakwal, Omagwa a jihar Ribas.
4. Filin dauka da tashin jiragen sama na Mallam Aminu Kano.
5. Filin sauka da tashin jiragen sama na Sam Mbakwe da ke Owerri.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Da yiwuwar za a dawo da zirga-zirga tsakanin jihohi a ranar 21 ga watan Yuni - Sani Aliyu "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?