--
Da duminsa: Ba zamu iya sayar da litan man fetur N121.5 ba - Yan kasuwan mai

Da duminsa: Ba zamu iya sayar da litan man fetur N121.5 ba - Yan kasuwan mai



ROHOTON: LEGIT.NG

Kungiyar yan kasuwar man fetur masu zaman kansu wato IPMAN, ta umurci mambobinta su sayar da litan man fetur a farashin N123.5 sabanin ragin da gwamnatin tarayya tayi na N121.5. IPMAN ta yi tsokacin haka ne kan sanarwan hukumar lura da farashin man fetur PPPRA da ta bada umurnin rage farashin, TheNation ta ruwaito.

Kungiyar yan kasuwar mai IPMAN ta ce kawai shawara gwamnati ta basu cewa su rage farashin ko kuma su cigaba da sayarwa a N123.5. Saboda haka, kungiyar ta umurci dukkan masu gidajen mai mambobinta su cigaba da sayar da man su a farashin N123.5 kafin kungiyar Depot su yanke shawara kan sabon farashin da gwamnati tayi umurni. Hakan na kunshe cikin sanarwan da shugaban kungiyar IPMAN, yankin jihar Kano, Alhaji Bashir Danmallam, ya saki ga manema labarai ranar Talata a Kano.

Ya ce dukkan yan kasuwan mai dake karkashinsa su bi shawarar ta hanyar da tabbatar da cewa ba'a sayar da litan mai fiye da N123.50 ba.

A jiya Litinin, Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa gwamnatin tarayya ta rage farashin litan mai a fadin Najeriya zuwa N121.50 sabanin N125.00 da ake sayarwa yanzu. Hukumar lura da farashin man fetur a Najeriya PPPRA ta yi sanarwa ne a wasikar da ta aikewa yan kasuwar mai a ranar Lahadi, 31 ga Mayu, 2020.

An ruwaito cewa an rage farashin man feturin ne sakamakon faduwar farashin danyen man fetur a kasuwar duniya da annobar COVID-19 ta haifar. Wannan shine karo na uku da za'a rage farashin man fetur cikin wannan shekarar. A ranar 18 ga Maris, gwamnatin tarayya ta sanar da ragin farashin litan mai daga N145 zuwa N125. Daga baya a ranar 31 ga Maris, an sanar da karin ragi daga N123.50 zuwa N125.00.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com



KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/






KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Da duminsa: Ba zamu iya sayar da litan man fetur N121.5 ba - Yan kasuwan mai"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?