--
COVID-19 ta kashe hadimi a fadar gwamnan Gombe, an rufeta ana shirin feshi

COVID-19 ta kashe hadimi a fadar gwamnan Gombe, an rufeta ana shirin feshi

ROHOTON: LEGIT.NG

Wani ma'aikacin gidan gwamnatin jihar Gombe ya rasu sakamakon annobar korona, lamarin da yasa aka rufe ofishin sakataren gwamnatin jihar tare da bada umarnin yin feshi a asibitin gidan. Shuaibu Danlami darakta ne na ayyuka na musamman da siyasa a ofishin sakataren gwamnatin jihar kuma ya rasu a ranar Lahadi bayan gajeriyar rashin lafiya,

kwamitin yaki da annobar korona ta jihar ta sanar. An diba samfur dinsa wanda sakamakon ya bayyana cewa yana dauke da cutar korona a ranar Talata, shugaban kwamitin, Idris Mohammed ya sanar a ranar Laraba.

Ya ce ofishin sakataren gwamnatin da gidan gwamnatin duk za a kulle su don yin feshi tare da daukar samfur din dukkan ma'aikatan don gwaji.

Danlami mamba ne kuma mataimakin sakataren kwamitin yaki da cutar na jihar kuma an dauka samfur din dukkan 'yan kwamitin. A halin yanzu, jami'ai na kokarin zakulo wadanda suka yi mu'amala da mamacin. Ana shirin zakulo su, yi musu gwaji da kuma killace duk wanda ya halarci jana'iza ko makokin Danlami. Danlami ne mutum na bakwai da ya rasu sakamakon annobar korona a jihar Gombe.

An sallami wasu mutum 125 daga cibiyar killacewa bayan warkewa da suka yi amma mutum 23 na cibiyar. Ya ce tunda mamacin mamba ne kwamitin yaki da cutar korona na jihar, za a tantance tare da yi wa 'yan kwamitin gwajin cutar.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com





KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/






KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "COVID-19 ta kashe hadimi a fadar gwamnan Gombe, an rufeta ana shirin feshi "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?