COVID-19: Nan da makonni kadan korona za ta yi kaura daga Kano - Jami'ai
Thursday, 4 June 2020
Comment
ROHOTON: LEGIT.NG
Shugaban kwamitin yaki da annobar korona ta jihar Kano, Dr Tijjani Hussein, ya bayyana cewa makonni kadan suka rage cutar ta yi kaura daga jihar Kano. Hussein, wanda ya bayyana hakan a yayin tattaunawa a kan inda aka kwana a kan cutar a jihar Kano a ranar Alhamis, ya yi kira ga mazauna jihar da su dauka matakan dakile yaduwar cutar.
Ya ce: "Idan mazauna jihar Kano za su kiyaye dokokin wanke hannu, saka takunkumin fuska da kuma nesa-nesa da juna, ina tabbatar da cewa nan da makonni kalilan za a nemi korona a Kano a rasa." Shugaban kwamitin ya kara da cewa, dukkan masu cutar da aka samu an samo su ne daga kananan hukumomi 30 na jihar amma kuma kashi 90% daga cikin masu cutar 'yan birnin Kano ne. Ya kara da cewa, kashi 76 na masu cutar a jihar maza ne inda kashi 24 suka kasance mata.
A martanin gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje ya ce sannu a hankali jihar ke koyon komawa walwalarta duk da cutar. Ya ce: "Da farko muna kallon lamarin a matsayin sabon abu wanda bamu taba sani ba. Amma a halin yanzu, mun san hanyar kamuwa da cutar da kuma hanyar kare kai." "Mun san hanyar wanke hannaye, nesa-nesa da juna da kuma saka takunkumin fuska. Idan muka ci gaba da bin doka, za mu kawo karshen annobar a Kano," ya kara da cewa.
A wani labari na daban, Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa a ranar Alhamis, 4 ga watan Yuni, ya tabbatar da mutuwar mutum hudu cif a jihar sakamakon annobar korona. Gwamnan ya bada wannan sanarwar ne a lafiya yayin taro da kwamitin yaki da cutar na jihar ta gudanar. Kamar yadda gwamnan ya bayyana,
cike da alhini yake sanar da mutuwar mutum hudu wanda suka hada da dan majalisar jihar mai wakiltar Nasarawa ta yamma daga cikin mutum 90 da suka kamu da cutar coronavirus a jihar. Gwamnan ya kara da cewa, samfur 705 aka kai wa hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya tun bayan da aka fara gwajin.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "COVID-19: Nan da makonni kadan korona za ta yi kaura daga Kano - Jami'ai "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?