--
Covid-19: Hukumar WAEC ta fadi lokacin zana jarabawar bana a Najeriya

Covid-19: Hukumar WAEC ta fadi lokacin zana jarabawar bana a Najeriya

ROHOTON: LEGIT.NG

Hukumar shirya jarawabar WAEC ta ce a shirye ta ke wajen gudanar da jarabawar bana a dukkanin makarantun sakandire da ke fadin Najeriya - Sai dai ta ce hakan ba zai tabbata ba har sai Gwamnatin Tarayya ta ba da izinin bude makarantu

 WAEC ta ce ko da an koma makarantu, ba za ta yi gaggawar gudanar da jarabawar ba Duk da yadda annobar cutar korona da dagula lamura da lissafi, Hukumar shirya jarabawar kammala karatun sakandire ta Yammacin Afrika WAEC, ta shirya gudanar da jarabawar a bana. Furucin hakan ya fito ne daga bakin Kakakin Hukumar, Demianus Ojijeogu, yayin ganawa da manema labarai a ranar Lahadi, 7 ga watan Yuni.

Hukumar za ta fara gudanar da jarabawa a bana da zarar Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ba da izinin bude makarantu a fadin kasar kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito.

Tun a watan Maris, Hukumar WAEC ta jingine shirinta na fara gudanar da jarabawar a bana, biyo bayan rufe kafatanin makarantu a fadin kasar yayin da gwamnati ta shimfida dokar kulle. Mista Demianus ya bayyana cewa, Hukumar a shirye ta ke ta fara gudanar da ayyukan da ta saba gudanarwa a kowace shekara, sai da ya ce ba ta cikin wani hanzari na aiwatar da hakan.

Ya ce da zarar gwamnati ta ba da izinin bude makarantu kuma dalibai sun koma aji, Hukumar WAEC za ta shimfida matakai da ka'idodin gudanar da jarabawar a bana. Ya na fatan cewa, Hukumar ba za ta hurawa dalibai wutar gaggauta gudanar da jarabawar ba duk da ta riga da yi musu tanadin kayayyakin karatu ta hanyar yanar gizo.

Ya ce WAEC za ta fitar da sabon jadawalin lokutan gudanar da jarabawar kuma yana da tabbacin sabon jadawalin zai ba dalibai isasshen lokacin da za su shirya. Haka kuma, za a bai wa malamai da shugabannin makarantu isasshen lokacin da za su kammala shirye-shiryensu gabanin jarabawar. Ya ci gaba da cewa, don neman kulawa da lafiyar dalibai da sauran masu ruwa da tsaki, WAEC za ta ba gwamnati damar tanadar amintattun cibiyoyi da makarantun gudanar da jarabawar.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/






KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Covid-19: Hukumar WAEC ta fadi lokacin zana jarabawar bana a Najeriya"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?