--
COVID-19: Akwai yuwuwar jihohi 32 su kasa biyan ma'aikata bayan annobar

COVID-19: Akwai yuwuwar jihohi 32 su kasa biyan ma'aikata bayan annobar



ROHOTON: LEGIT.NG

Wani kwararre a fannin tsari da shugabanci, Dr. Tunji Ogunyemi, ya ce a kalla jihohi 32 ne za su kasa biyan albashi bayan annobar korona ta wuce. Ya ce akwai yuwuwar a sake duba kasafin kudin Najeriya bayan wannan zabtarewar da aka yi sakamakon abinda ke faruwa a fadin duniya.


Masanin tattalin arzikin kuma lauya wanda yake mukaddashin shugaban sashen karantar tarihi na jami'ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife, ya yi kira ga gwamnati da ta hadu da shugabannin kwadago don kara duba takardar da kwamitin Kwamared Hassan Sunmonu ya fitar.

Ya ce jihar za ta fuskanci babban kalubale bayan annobar korona ta tafi.

Ogunyemi, wanda ya tattauna da wani gidan rediyo da ke Osogbo, ya ce: "Gwamnatin tarayya za ta iya hanzarta wa wurin buga kudade don biyan ma'aikata ba sai ta jira sun samu ta wani wuri ba.

"Amma babu jihar da za ta iya yin haka. Tuni jihohi ke suka zabtare kasafin kudin su saboda raguwar tallafi daga gwamnatin tarayya. "Abinda jihohi za su samu a watan Yuni zai zama rabin wanda aka samu a watan Janairu. Jihohi hudu ne kacal za su samu daidaito.

"Damar da ma'aikatan gwamnati suke da ita yanzu shine babu wanda zai ce su tafi ba zai biya ba. Amma jihohi za su iya zabtare albashinsu saboda ba za su iya biya ba. Za su iya biyan ma'aikata ne da abinda suke da shi. "A halin yanzu, jihohi irin su Kaduna, Delta, Filato, Taraba da Gombe duk sun zabtare albashin ma'aikatan su."

Ya kara da cewa, "Babban kalubale ne ke tunkarar mu kai tsaye, sai mun kwashe shekaru biyar a jere kafin mu koma daidai." A wani labarin kuma, Legit.ng ta rahoto a baya cewa kamfanin man fetur ta kasa (NNPC) ta ce ta samar da manhajar zakulo wadanda suka yi ma'amala da masu cutar korona wacce za a iya amfani da ita a sassa daban-daban na fadin kasar nan.



KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/






KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "COVID-19: Akwai yuwuwar jihohi 32 su kasa biyan ma'aikata bayan annobar "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?