--
Arziki Kashi: Jerin baƙaƙen fata 15 mafi arziki a duniya

Arziki Kashi: Jerin baƙaƙen fata 15 mafi arziki a duniya

ROHOTON: LEGIT.NG

'Yan Najeriya hudu sun shiga jerin bakaken fatar da suka fi kowa kudi a duniya - Aliko Dangote ya kasan ce daya daga cikin mutanen da suka hau sahun masu kudin tare da Will Smith, Mike Jordan, Oprah Winfrey

- Macen Najeriya da ta shiga cikin jerin bakaken fatar masu kudi ita ce Folorunsho Alakija, wadda ta mallaki dala biyliyan (N387,500,000,000) 'Yan Najeriya hudu sun sake zama abun alfahari ga kasar su yayin da suka fito a cikin sahun bakaken fata masu kudi na duniya kamar yadda Africa Facts Zone ta fitar.

Cikin jerin wanda Africa Facts Zone ta wallafa a shafin sadarwa na Twitter, Dangote shi ne ya jagoranci tawagar attajiran yayin da adadin dukiyar da ya mallaka ta kai $9.5bn (N3,676,500,000,000).

Mike Adenuga ya kasance a mataki na uku a jerin bakaken masu arziki, inda ya mallaki $5.8bn. Na uku a cikin 'yan Najeriya da suka jerin shi ne, Abdussamad Rabi'u, wanda ya fito a sahu na shida cikin jerin attajiran.

Adadin dukiyarsa ta kai dala biliyan 3.2 (N1,240,000,000,000). Sai kuma ta hudu, Folorunsha Alakija, a sahu na 14 cikin jerin biyo bayan dala biliyan 1 da ta mallaka, kimanin N387,500,000,000 kenan a kudin Najeriya.

Shahararriyar mai shirin nan na The Oprah show, Oprah Winfrey, da kuma fitaccen jarumi, Will Smith, sun haye sahu na bakwa da na hudu. Winfrey tana dukiya wadda adadin ya kai dala biliyan 2.6. Haka shi ma jarumin, Will Smith, ya na da dukiya da adadin ta ya kai dala biliyan 5.

Ga dai jerin bakaken attajirai 15 mafi arziki a fadin duniya, kasashen da suka fito da kuma adadin dukiyar da kowanensu ya mallaka:

 1. Aliko Dangote (Najeriya) - $9.5 billion

2. Mohammed Hussein (Saudiya) - $8.1 billion

 3. Mike Adenuga (Najeriya) - $5.8 billion

4. Will Smith (Amurka) - $5 billion

5. David Steward (Amurka) - $3.5 bn

6. Abdul Samad Rabiu (Najeriya) - $3.2 bn

7. Oprah Winfrey (Amurka) $2.6 bn

8. Mike Jordan (Amurka) - $2.1 bn

9. Patrice Motsepe (Afrika ta Kudu) - $2bn

10. Isabel Dos Santos (Angola) - $1.8bn

11. Strive Masiyiwa (Zimbabwe),

 Michael Lee-Chin (Canada da Jamaica) - $1.7 bn

13. Kanye Omari West (Amurka) - $1.3 bn

14. Folorunsho Alakija (Najeriya) - $1 bn

15. Shawn Corey Carter wanda aka fi sani da Jay-Z (Amurka) - $1 bn



KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/






KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Arziki Kashi: Jerin baƙaƙen fata 15 mafi arziki a duniya"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?