
Alburusai 818 cikin shinkafa: Wasu mata 3 sun fada komar Yan sanda (Bidiyo)
Saturday, 27 June 2020
Comment
Rundunar 'Yan sandan Najeriya ta yi holen wasu mata uku da aka kama bayan gano alburusai 818 da aka boye cikin buhun shinkafa. Matan dai sun hada da Eleana Yowei mai shekara 25, Favour Bello mai shekara 21 da Priye Jimi mai shekara 30. Lance Corporal Yowei,
mijin Eleana Yowei shima a halin yanzu yana tsare a hannun Rundunar Sojojin Najeriya. Eleana ta shaidawa manema labarai cewa mijinta, Lance Corporal Yowei ne ya kawo buhun masarar gida daga Zamfara.
Ta ce mijinta da su ka yi shekara 7 da aure ya kira ta a waya a ranar 28 ga watan Mayu inda ya ce Favour Bello wacce ke zaune tare da ita za ta tafi Bayelsa kuma ta bata buhun shinkafar ta tafo da shi. Ya kara da cewa Favour za ta ba wa mahaifiyarta, Priye Jimi, shinkafar idan ta isa jihar Bayelsa.
Bayan kwana daya, mijinta ya kira ta ya fada mata cewa ma'aikatan tashan mota sun rike Favour. Ya aike sojoji daga bariki su bi sahun ta amma suka aka tsare su. A yammacin ranar 'yan sanda suka tafi gida suka kama ta. An kai ta ofishin SARS da ke Bompai, Kano inda aka tsare ta na sati daya sannan aka tafi da uita birnin tarayya, Abuja.
Cikin hawaye, Eleana ta shaida wa manema labarai cewa ba ta duba abinda ke cikin buhun shinkafar ba domin ta yarda da mijinta. Ta ce tsautsayi ne ya fada kanta kuma ta shawarci mutane su rika duba duk wani kaya da aka basu ajiye ko sako.
Kakakin Rundunar Yan sanda, DCP Frank Mba yayin taron manema labaran ya ce an gano alburusan da aka boye cikin shinkafar ne a tashan mota a Kano. Ya shawarci yan Najeriya su guji kwadayi da hanzarin samun kudi ta ko wane hali.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Alburusai 818 cikin shinkafa: Wasu mata 3 sun fada komar Yan sanda (Bidiyo) "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?