
Ahmad Lawan: Abin da ya sa Najeriya ta gaza cin yaki da ‘yan ta’adda
Wednesday, 10 June 2020
Comment
ROHOTON: LEGIT.NG
Lawan ya ke cewa rashin samun manyan makaman da ake bukata ya kawowa jami’an tsaro cikas. Da ya ke yi wa manema labarai bayani, sanata Dr. Ahmad Lawan ya ce ana batawa dakarun sojojin Najeriya lokaci fiye da yadda ya kamata kafin su iya fansar makaman yaki. Shugaban majalisar ya ke cewa aiki ya yi sojojin Najeriya yawa, sannan kuma akwai bukatar a tanadi kayan yaki kafin a iya shawo kan matsalar rashin tsaron da ake fama da shi.
“Kusan ka iya cewa mu na fama da matsalar siyasar Duniya. Na san cewa wajen kokarin sayen kayan jiragen yaki, ya kan dauke mu tsawon lokacin watanni shida ko ma tara.”
Sanatan ya ce akwai rashin adalaci harkar ta ke tafiya: “Idan wata kasar ta rubutawa gwamnati takarda cewa ta na son makamai, sai a saida mata a cikin wata guda ko kuma biyu.” “Saboda haka abubuwa ba su tafiya daidai, wannan ya na cikin kalubalen mu. Za mu cigaba da kokarin tattaunawa da wadannan kasashe da ba su gane inda mu ka dosa ba.”
“Jami’an tsaronmu kuma su na bukatar karin dakaru da kudi.” “Mu na bukatar karin jami’an ‘yan sanda, masu kula da shige da fice da kusan duk wasu bangarorin tsaro.” Dr. Lawan ya ke cewa Najeriya ta na kuma da bukatar ma’aikata. “Gwamnati ta na bakin kokari wajen samun kayan aiki da makamai.”
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Ahmad Lawan: Abin da ya sa Najeriya ta gaza cin yaki da ‘yan ta’adda "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?