
A karshe dai masana a Najeriya sun gano maganin cutar Coronavirus
Thursday, 25 June 2020
Comment
Masanan jami’o’in Najeriya sun gano maganin cutar coronavirus.
Masanan sun bayyana hakane a ranar Juma’ar da ta gabata 19 ga watan Yuni, inda suka ce sun samar da maganin ne a Afrika kuma ga ‘yan Afrika, amma zai yi aiki a wasu sassa na duniya idan an fitar dashi, The Guardian ta ruwaito.
Shafin Press Lives ta rawaito cewa ta gano shugaban kungiyar masanan Dr Oladipo Kolawole, ya ce za a dauki watanni 18 kafin a fitar da maganin ga jama’a.
Ya ce hakan ya biyo bayan bincike, nazari da kuma neman amincewar hukumomi kan amfani da maganin.
Kolawole ya ce nazarin da suka yi wanda ya basu damar samar da wannan magani, sun kashe kimanin naira miliyan bakwai da digo takwas (N7.8m).
A wani rahoton makamancin haka kuma, wata kungiyar masu bin addinin Katolika na Najeriya sun sanar da samar da maganin cutar na COVID-19, wanda suka kira shi da suna ‘Pax CVD Plus’.
Wata sanarwa da ta fito dauke da sa hannun shugaban su Anselm Adodo OSB, a ranar Laraba 29 ga watan Afrilu, ita ce ta bayyana haka. Shugaban ya ce maganin an samar da shi ne domin warkar da cutar Coronavirus.
Anselm ya ce maganin da suka samar da shi daga itatuwa, shine abinda yafi da cewa saboda yana da saukin hadawa, ajiyewa da kuma rabawa, sannan kuma duka masana lafiya da wadanda ba masana ba za su iya amfani da maganin saboda bashi da wata illa sosai.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "A karshe dai masana a Najeriya sun gano maganin cutar Coronavirus"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?