
Yanzu-yanzu: Sabbin Mutane 146 sun kamu da Coronavirus, Legas da Kano a gaba
Tuesday, 12 May 2020
Comment
Hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa a kasa (NCDC) ta ce annobar cutar covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 146 a fadin Najeriya. Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11:55 na yammacin ranar Talata, 12 ga watan Mayu, 2020.
A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na tuwita, ta sanar da cewa karin sabbin mutane 146 din sun fito daga jihohin Najeriya kamar haka;
57-Lagos, 27-Kano, 10-Kwara, 9-Edo, 8-Bauchi, 7-Yobe, 4-Kebbi, 4-Oyo, 3-Katsina, 3-Niger, 2-Plateau, 2-Borno, 2-Sokoto, 2-Benue, 1-Gombe, 1-Enugu, 1-Ebonyi, 1-Ogun, 1-FCT, 1-Rivers
A yau, an sallami mutane 57 bayan sun samu waraka kuma an yi rashin mutane 8.
146 new cases of #COVID19;— NCDC (@NCDCgov) May 12, 2020
57-Lagos
27-Kano
10-Kwara
9-Edo
8-Bauchi
7-Yobe
4-Kebbi
4-Oyo
3-Katsina
3-Niger
2-Plateau
2-Borno
2-Sokoto
2-Benue
1-Gombe
1-Enugu
1-Ebonyi
1-Ogun
1-FCT
1-Rivers
4787 cases of #COVID19 in Nigeria
Discharged: 959
Deaths: 158 pic.twitter.com/vlqzSxqacq
NCDC ta ce ya zuwa karfe 11:55 na yammacin ranar Talata, 12 ga watan Mayu, akwai jimillar mutane 4787 da aka tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar covid-19 a fadin Najeriya.
An sallami mutane 959 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 158. l
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Yanzu-yanzu: Sabbin Mutane 146 sun kamu da Coronavirus, Legas da Kano a gaba "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?