'Yan bindiga sun budewa shugaban jam'iyyar APC wuta yayin da ya ziyarci kauyensu a Katsina
Sunday, 31 May 2020
Comment
ROHOTON: LEGIT.NG
'Yan bindiga a jihar Katsina sun kashe shugaban jam'iyyar APC na karamar hukumar Batsari, Abdulhamid Sani Ruma, a kauyensu. Ruma ya gamu da ajalinsa ne yayin da ya ziyarci kauyensu, Sabon Garin Dunburawa, domin jagorantar rabon gado ga 'ya'yan dan uwansa da 'yan bindiga su ka kashe a shekarar da ta gabata.
Wata majiya ta sanar da Daily Trust cewa wasu 'yan bindiga ne a kan babura, da su ka fito daga jeji, su ka da budewa Ruma wuta, inda ya mutu nan take. Likitoci sun tabbatar da mutuwarsa bayan an kai gawarsa babban asibitin karamar hukmar Batsari "Ya bar kauyen nan da misalin karfe 9:00 na safe domin komawa gidansa da ke garin Batsari. Kilomita hudu ne daga kauyen Sabon Garin Dunburawa zuwa garin Batsari.
"Shi kadai aka harbe a cikin mutanen da su ke tare," a cewar majiyar Daily Trust. Mataimakin shugaban jam'iyyar APC na mazabar Katsina ta tsakiya, Mamman Yaro Batsari, ya tabbatar da kisan Ruma. Ya ce batun kisan Ruma da 'yan bindigar su ka yi, ya jefa jama'a cikin firgici.
"A irin wannan lokacin 'yan bindiga su ka kashe dan uwansa shekarar da ta gabata, yanzu kuma shi ma su ka kashe shi bayan ya ziyarci kauyensu domin rabon gadon dan uwan nasa da aka kashe "Ya na cikin gonaki yayin rabon gadon ne sai wasu 'yan bindiga su ka bullo daga cikin jeji su ka bude ma sa wuta. "Shi kadai su ka harba,
sun harbe shi a ka da kirji. Yanzu haka an dauki gawarsa zuwa gidansa domin yi ma sa jana'iza," a cewarsa. Har ya zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, rundunar 'yan sandan jihar Katsina ba ta ce komai ba a kan faruwar lamarin.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "'Yan bindiga sun budewa shugaban jam'iyyar APC wuta yayin da ya ziyarci kauyensu a Katsina "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?