
'Yan bindiga sanye da hijabi sun sace basarake a Nasarawa
Saturday, 2 May 2020
Comment
Daya daga cikin danginsa ya shaidawa Daily Nigerian a ranar Asabar cewa yan bindigan sun yi awon gaba da basaraken a kan babur kuma kawo yanzu ba a san inda suka tafi da shi ba. Majiyar ya ce masu garkuwa da mutanen da adadin su ya tasanma 20 sun iso ne dauke da muggan makamai.
A cewar majiyar, wasu daga cikin yan bindigan sun saka hijabi, sannan suka haura katangan fadar sarkin kafin suka gano inda ya ke.
Masu garkuwa da mutanen sun tuntubi iyalan sarkin sun nemi a biya su kudin fansa ta Naira miliyan 50. Majiyar ta kara da cewa masu garkuwa da mutanen sun bawa sarkin dama ya yi magana da iyalansa a safiyar ranar Asabar, kwanaki biyu bayan sace shi.
"Ya kira safiyar yau ya ce suna neman a biya su Naira miliyan 50 kafin su sake shi. "Sun tafi da wayar dansa sannan su ka kira wani lamba da suka gani a cikin wayar shi kuma ya zo ya zo gidan sarkin ya shaida musu cewa sun yi magana kuma sun ce a biya su Naira miliyan 50,"
a cewar majiyar. Daily Nigerian ta yi kokarin ji ta bakin Rundunar Yan sanda game da sace basaraken amma Kakakin yan sandan, Nansel Ramhnan bai amsa wayarsa ba a lokacin da aka hada wannan rahoton.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP
0 Response to "'Yan bindiga sanye da hijabi sun sace basarake a Nasarawa"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?