YADDA ZAKA BUDE ACCOUNT DIN BANKI NA GTBANK DA WAYAR KA
Sunday, 31 May 2020
Comment
Duba da matukar amfanin account din banki, a
yau naga ya dace mu yi ma mutane dan
takaitaccen bayanin yadda zasu iya bude
Account din banki da kan su alhali suna gida a
kwanciyar su ba tare da wani wahala ba.
yau naga ya dace mu yi ma mutane dan
takaitaccen bayanin yadda zasu iya bude
Account din banki da kan su alhali suna gida a
kwanciyar su ba tare da wani wahala ba.
A yau
kusan ko me kake son yi idan baka da bank
account sai kaga abin yana nema yafi karfin ka.
Ya ishe ka misali har yanzu maganar da nake
maka akwai wadanda ke karkashin tsarin Npower
kusan cikin shekara ta biyu suke amma har
yanzu basu fara karbar ko sisin kwabo ba,
kasancewar rashin takamaimai din account din
banki.
Mafiya yawan wadanda suka gamu da
wannan matsalar kodai ya kasance sun yi amfani
da Account number din wani, ko kuma account
din da suka sanya ya lalace wato ya zama
dormant.
A wannan zamanin ina mamakin ganin matashi
cikakke wanda ya kai kimanin shekara ashirin
abinda yayi sama wai baya da bank account.
Mu
sani bank account ba lallai sai ma'aikata ko
masu wani yawan transactions na kudi bane
kawai ke iya bude Account kowa zai iya budewa
saboda tsaro dani gudun ko ta kwana.
Ba tare da bata lokaci ba zan tafi kai tsaye kan
yadda zaka bude Account din cikin sauki ta
hanyar amfani da wayar ka ta hannu ko ma wace
iri ce kai in takaice maka koda kuwa Nokia
torchlight ce.
Ga wanda yake bukatar bude Account na
GTBANK sai kawai ya latsa *737# ya sanya kira.
Bayan tayi loading zasu bashi menu kamar haka
1. Airtime-self
2. Airtime-others
3. Buy data
4. Transfer funds GTBANK
5. Transfer funds other banks
6. Account Balance
7. Create/change pin
8. Next
To anan ba tare da bata lokaci ba sai a latsa 8
sannan ka sanya OK na wayar ka.
Zai bude maka
wani fejin mai kama da na sama kamar haka:
1. Cardless withdrawal
2. Open account
3. Cheque status
4. Salary advance
5. Loan balance
6. Generate token
7. Deposit and withdrawal
Anan sai kayi reply da 2 sai ka sanya Okey. Zasu
sake baka options kamar haka:
1. Used BVN details
2. Supply details
Idan kana da BVN already sai kawai ka danna 1
tare da OK.
Nan take zasu yi searching din BVN
details naka kamar suna, shekarar haihuwa,
lambar waya, address, hoto tare da finger print.
Ba tare da wani bata lokaci ba zasu aiko maka
da Account number din ka cikin abinda bai wuce
minti biyu ba.
Daga sun turo maka account
number Shikenan ka kammala bude Account
dinka sai kawai ka fara enjoying duk services din
da bankin yake rendering ga abokan huddar su.
GA WANDA BAYA DA BVN KUMA
Idan suka baka wannan option din:
1. Used BVN details
2. Supply details
Sai ka danna 2 ka sanya OK zasu kai ka feji na
gaba mai dauke da option kamar haka:
"ENTER FIRST NAME"
Sai ka rubuta sunan ka sai ka danna OK zai kai
ka wani feji kamar haka:
"ENTER LAST NAME "
Sai ka rubuta sunan mahaifin ka, sai ka danna
OK.
Zasu bude maka wani feji haka:
"Do you have a middle name"
1. Yes
2. No
Wato kana da wani sunan bayan wadannan,
ma'ana idan da suna uku kake bearing sai ka
danna 1 sai danna OK zasu umarci ka sanya
dayan sunan sai ka latsa OK. Idan kuma da suna
biyu kake bearing sai kawai ka danna 2 ka danna
OK.
Daga nan zasu kai ka wani fejin kamar haka.
"Please select your gender"
1. Male
2. Female
Anan jinsin ka ake bukata kayi specifying sai
maza su sanya 1 su danna OK, su kuma mata su
danna 2 su sanya OK.
Daga nan zasu tambaye
ka DOB din ka ma'ana date of birth din ka Sai ka
cike appropriately.
Kana gama cike wadannan details din zasu aiko
maka da account number dinka.
A wannan
lokacin ma zaka iya antaya ma account din kudi
don ajiya, sai dai ba zaka cirewa ba har sai kaje
banki kayi enrollment na BVN tare da passport
photograph da kuma national ID card, ko Tax
identification ID, ko voters card.
Shikenan...
Me tambaya yayi a karkashin wajen tura sako ta email, mai
sharing ko copying ma yayi amma lallai ya
bayyana ya kwafo daga shafin mu ne.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "YADDA ZAKA BUDE ACCOUNT DIN BANKI NA GTBANK DA WAYAR KA"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?