--
Nijar za ta fara tatsar bayanan mutane a wayoyin salula

Nijar za ta fara tatsar bayanan mutane a wayoyin salula



A Jamhuriyar Nijar, majalisar dokokin ƙasar ta amince da wata dokar da za ta bai wa hukumomi damar sauraren maganganun 'yan kasar ta wayoyi ko kafofin sadarwar zamani.

A halin yanzu, za a iya amfani da muryoyin mutane da aka naɗa yayin da suke yin waya wurin gudanar da bincike.

Nijar na ɗaya daga cikin ƙasashen Afirka da ke fama da hare-haren masu iƙirarin jihadi.

Ƙudurin dokar ya samu amincewa da ƙuri'a 104 cikin 'yan majalisa 171 na ƙasar. 'Yan majalisa na ɓangaren adawa sun fice daga zauren majalisar lokacin kaɗa ƙuri'ar don nuna rashin amincewarsu da wannan doka.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Nijar za ta fara tatsar bayanan mutane a wayoyin salula"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?