
Mutuwar sarki: Matawalle ya nada madadin marigayi Sarkin Kauran Namoda
Wednesday, 6 May 2020
Comment
ROHOTON: https://hausa.legit.ng/news/
Bello Mohammed Matawallen Maradun, gwamnan jihar Zamfara, ya nada Alhaji Sanusi Mohammed a matsayin sabon sarkin masarautar Kauran Namoda. Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da Zailani Baffa, kakakin gwamnan jihar Zamfara, ya fitar da yammacin ranar Laraba. Ya ce gwamnan ya zabi Mohammed a matsayin sabon sarki bisa shawarar ma su ruwa da tsaki a nadin sabon sarki a masarautar Kauran Namoda.
Sabon sarkin ya maye gurbin tsohon sarki Alhaji Mohammed Ahmed Asha wanda Allah ya yi wa rasuwa ranar Lahadi, 03 ga watan Mayu, 2020. Kafin nadinsa a matsayin sabon sarki, Mohammed, mai shekaru 40 a duniya, manjo ne a rundunar sojin Najeriya. Mohammed da ne wurin marigayi Asha, kuma shi ne sarkin yanka na biyu a tsarin sarki mai sanda a masarautar, amma ku ma sarki na 16 a tsarin masarautar Kiyawan Kauran Namoda.
Da safiyar ranar Lahadi ne Legit.ng ta wallafa labarin mutuwar Sarkin masarautar Kauran Namoda a jihar Zamfara, Alhaji Muhammad Ahmad Asha. Sarkin ya rasu ne da safiyar ranar Lahadi, 3 ga watan Mayun 2020 bayan fama da gajeriyar rashin lafiya kamar yadda wani na kusa da fadar sarkin ya tabbatar wa BBC.
Ya rasu yana da shekaru 71 a duniya, ya kuma bar mata uku da yaya da dama. A cewar jaridar The Punch, Sarkin ya mutu ne a asibitin da aka killace shi. Jaridar ta ce ya ana zargin cewa cutar covid-19 ce ta yi sanadin mutuwarsa. The Punch ta ce sakataren yada labarai na kwamitin yaki da cutar covid-19 a jihar Zamfara, Mustafa Jafaru,
ya ce basaraken ya na killace ne a asibitin kwararru da ke garin Gusau, babban birnin jiha. Jafaru ya bayyana cewa an dauki jininsa tare da aika shi zuwa dakin gwaji a Abuja, amma har ya zuwa yanzu sakamakon gwajin bai fito ba. Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sani Yariman Bakura, ne ya nada marigayin a matsayin sarki mai sanda na masarautar Kauran Namoda a shekarar 2004.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP
0 Response to "Mutuwar sarki: Matawalle ya nada madadin marigayi Sarkin Kauran Namoda "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?