--
Mutanen Kaduna na mutuwa a gidajensu saboda ka kulle su a gida – Jama’atul Nasril Islam ta sanar da El-Rufai

Mutanen Kaduna na mutuwa a gidajensu saboda ka kulle su a gida – Jama’atul Nasril Islam ta sanar da El-Rufai

A jiya Asabar ne kungiyar Jama’atul Nasril Islam dake Zaria, ta bayyana akwai yawaitar mace-mace da ake samu a jihar Kaduna saboda dokar hana zirga-zirga da gwamnatin jihar ta sanya.

Kungiyar ta bayyana hakane ga manema labarai ta bakin shugaban kungiyar Abdullahi Yahaya da sakataren kungiyar Mahmud A. Abdullahi.

Yahaya ya ce mutanen dake fama da rashin lafiya wacce ba ta da alaka da Coronavirus ba a yi musu magani saboda dokar hana zirga-zirga da aka sanya.

Ya ce idan har an sanya dokar ne saboda a ceto rayuwar al’umma, rayuwar mutane na ta salwanta a kowacce rana inda yawansu yafi na wadanda suke mutuwa saboda cutar Coronavirus.

“Yawan mutanen da suke mutuwa saboda basa samun cikakkiyar kulawa a asibiti abin babu dadin ji. Yawancinsu kuma jarirai ne da mata masu ciki. Hakan ya samo asali saboda gwamnati ta kasa samo hanyar da za ta kare rayukan al’umma.

“Mutane da yawa sun shiga wani hali, an hana manoma zuwa gona; ‘yan kasuwa na cikin wani hali saboda an hana su bude shagunansu, asibitoci da yawa an mayar da su wajen duba masu cutar Coronavirus, bayan haka babu wani taimako da ake yiwa talakawa don inganta rayuwarsu.”

Yahaya ya ce mutane da yawa suna cikin tashin hankali, saboda an dakile musu hanyar samun na abinci, ya zama basu da wata hanyar da za su iya samun kudi su ciyar da iyalansu.

Ya ce gwamnatin jihar na bukatar tayi tunani akan wannan lamari na hana zirga-zirga, inda yace yawan mutanen da suke mutuwa a kullum saboda dokar hana zirga-zirgar yafi wadanda suke mutuwa saboda Coronavirus a jihar.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/



KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Mutanen Kaduna na mutuwa a gidajensu saboda ka kulle su a gida – Jama’atul Nasril Islam ta sanar da El-Rufai"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?