
'Mun kama jirgin Burtaniya mai fasakaurin jama'a zuwa Najeriya'
Monday, 18 May 2020
Comment
Gwamnatin Najeriya ta ce ta kama wani jirgin sama mallakar wani kamfani da ke Burtaniya bisa zarginsa da yin jigilar Fasinjoji zuwa cikin kasar duk da hanin da aka saka na yin hakan saboda annobar korona.
Ministan sufurin jiragen sama na kasar Hadi Sirika wanda ya sanar da hakan, ya ce an ba jirgin na kamfanin Flair Aviation ne iznin jigila zuwa cikin kasar don taimaka wa wajen ayyukan jinkai, amma kuma ya fake da hakan wajen soma jigila irin ta kasuwanci.
Hadi Sirika ya kara da cewa abin ya ba su mamaki inda suka tsare jirgin sannan ana gudanar da bincike domin gano hakikanin abin da ke faruwa.
COVID-19. Flair Aviation, a UK company, was given approval for humanitarian operations but regrettably we caught them conducting commercial flights. This is callous! The craft is impounded, crew being interrogated. There shall be maximum penalty. Wrong time to try our resolve!🇳🇬— Hadi Sirika (@hadisirika) May 17, 2020
Ministan dai ya yi zargin abin da ya kira "suna bincike domin gano ko akwai wani abu da ake rufe musu kuma idan muka same kamfanin da laifi za mu hukunta shi daidai gwargwado." Ya ce gwamnatin Najeriya ta yi shigar burtu inda ta gano yawan kudin da ake biyan jirgin domin kai jama'a Najeriya.
Sai dai kuma ministan bai fadi tsawon lokacin da jirgin ya kwashe yana gudanar da 'haramtattun ayyukan' da gwamantin Najeriyar ke zargin kamfanin.
Har kawo yanzu dai kamfanin Flair Aviation bai ce uffan ba dangane da zargin kuma da zarar ya mayar da martani za mu sanar da jama'a.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "'Mun kama jirgin Burtaniya mai fasakaurin jama'a zuwa Najeriya'"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?