Manyan ‘Yan wasan kwallon Duniya da su ka kamu da cutar COVID-19
Saturday, 2 May 2020
Comment
- Kusan mutum miliyan uku da rabi su ka kamu da Coronavirus a Duniya Cutar COVID-19 ba ta bar manyan taurari irinsu ‘yan wasan kwallon kafa ba,
- Garay, Dybala, da Felliani su na cikin wadanda da cutar COVID-19 ta kama
Jaridar Punch ta fito da rahoto dauke da sunayen ‘yan wasan kwallon kafa su ka kamu da cutar.
Daga ciki akwai:
1. Callum Hudson-Odoi A tsakiyar watan Maris aka tabbatar da cewa matashin ‘dan wasan Chelsea, Callum Hudson-Odoi ya kamu da cutar Coronavirus.
2. Ezequiel Garay Kwanaki kungiyar Valencia ta tabbatar da cewa Ezequiel Garay ya na dauke da COVID-19. Sauran wadanda aka samu da cutar sun hada da Eliaquim Mangala.
3. Ekdal, La Gumina, Thorsby, Depaoli da Bereszynski7 A kungiyar Sampodoria an samu ‘yan wasa da-dama da cutar ta kama. Daga ciki akwai Albin Ekdal, Antonino La Gumina, Morten Thorsby, Fabio Depaoli da Bartosz Bereszynski.
Haka zalika cutar ta kama wani babban jami’in kulon din mai suna Amedeo Baldari.
4. Maldini Tsohon ‘dan wasan AC Milan, Paolo Maldini ya kamu da wannan cuta kwanaki amma daga baya ya samu lafiya. ‘Dansa ‘dan wasa Daniel Maldini shi ma ya yi jinyar cutar a Italiya.
5. Luca Kilian A cikin ‘yan wasan kasar Jamus, ‘dan wasan kungiyar Paderborn Luca Kilian ne ya fara kamuwa da Coronavirus.
6. Timo Hubers A watan jiya sakamakon gwaji ya nuna cewa ‘dan wasan bayan Hannover, Timo Hubers ya kamu da COVID-19 bayan ya halarci wani taron biki.
7. Paul Akpan Udoh Paul Udoh ‘dan wasa ne da ke bugawa wata karamar kungiyar kwallon kafa mai suna Pianese da ke Italiya. Ainihinsa ruwa-biyu ne; ‘dan Najeriya da kasar Italiya, ya kamu da cutar.
8. Paulo Dybala. Tauraro Paulo Dybala ya na fama da cutar COVID-19 har yanzu bayan watanni da kamuwa da ita. Sai dai Budurwarsa ta karyata rade-radin cewa har yanzu ta na asibiti.
9. Maroune Felliani A daf da karshen watan Maris ne aka samu labarin cewa ‘dan wasa Marouane Fellaini mai shekara 32 ya kamu da COVID-19. ‘Dan kwallon ya warke bayan kwanaki a asibiti a Sin.
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP
0 Response to "Manyan ‘Yan wasan kwallon Duniya da su ka kamu da cutar COVID-19"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?