
Manyan kabilu 10 da suka fi shahara a nahiyar Afrika
Thursday, 28 May 2020
Comment
ROHOTON: LEGIT.NG
Ubangiji ya albarkaci nahiyar Afrika da mutane hazaikai da kuma kabilu masu tarin yawa. Legit.ng ta tattara muku kabilu daban-daban da suka fi jama’a masu tarin yawa a nahiyar Afrika. Ga jerin kabilu 10 a nahiyar Afrika da suka fi kowacce kabila yawa kamar yadda Facts one ta bayyana.
1. Kabilar Hausa - miliyan 78: Tana da mutane a kalla miliyan 78 a fadin nahiyar Afrika. Ana samu masu yin yaren a kasashe masu tarin yawa na fadin haiyar.
2. Igbo - miliyan 45: Da mutum miliyan 45 ne kabilar Ibo ta zama ta biyu a cikin kabilu mafi yawan mutane a nahiyar Afrika.
3. Yoruba - miliyan 44: Kabilar nan ce ke biye da kabilar Ibo a yawan mutane a nahiyar Afrika. Tana da mutane masu yawan miliyan 44.
4. Oromo - miliyan 40: Kabilar Oromo ce kabila ta hudu a yawan jama’a a nahiyar Afrika. Tana da mutum miliyan 40.
5. Fulani - miliyan 35: Kabilar Fulani ce ta biyar a wannan jerin, tana da mutane miliyan 35 a nahiyar Afrika.
6. Amhara - miliyan 20.2: Kabilar ce ta shida a wannan jerin kuma tana da jama’a miliyan 20.2
7. Akan - miliyan 20: Akan kabila ce da ke da yawan mutane har miliyan 20 a fadin nahiyar Afrika.
8. Somali - miliyan 20: Kabilar Somali c eke biye da Akan wacce ke da miliyan 20 na jama’a.
9. Hutu - miliyan 18.5: Kabilar tana da jama’a miliyan 18.5 na masu yin yarenta a Afrika.
10. Ijaw - miliyan 15: Kabilar Ijaw ce ta karshe kuma ta goma a wannan jerin. Tana da mutane miliyan 15 da ke yin yaren a Afrika.
A baya mun kawo cewa, yaren Hausa ne yaren da aka fi yi kuma mafi dadewa a cikin yankin mutane miliyan 120 kamar yadda aka gano. Masu yin yaren na nan dankam a kasashen Najeriya, Nijar, Chadi, jamhuriyar Benin, Kamaru, Togo, jamhuriyar Afrika ta tsakiya, Ghana, Sudan, Eritrea, Guinea, Gabon, Senegal da Gambia.Africa's Most Populous Ethnic Groups (Worldwide)— Africa Facts Zone (@AfricaFactsZone) May 28, 2020
1. Hausa - 78 million
2. Igbo - 45 million
3. Yoruba - 44 million
4. Oromo - 40 million
5. Fulani - 35 million
6. Amhara - 20.2 million
7. Akan - 20 million
Somali - 20 million
9. Hutu - 18.5 million
10. Ijaw - 15 mil
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Manyan kabilu 10 da suka fi shahara a nahiyar Afrika"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?