
Mace-macen Kano: Allah ya yi wa tsohon Jarman Kano rasuwa
Sunday, 3 May 2020
Comment
Kasa da sa'o'i 24 bayan rasuwar Tafida Abubakar, sarkin Rano na jihar Kano, jihar ta kara yin wata babbar rashi. Isa Hashim, farfesa mai murabus wanda ya rike sarautar Jarman Kano a masarautar Kano, ya rasu a safiyar Lahadi, kamar yadda majiya daga iyalan mamacin ta tabbatar. Tsohon farfesan mai shekaru 84 ya rasu a gidansa ne sakamakon gajeriyar rashin lafiya,
diyarsa mai suna Dija Hashim ta sanar da jaridar Premium Times. Har yanzu babu bayanai a kan ciwon da ya kashe shi. Amma iyalansa sun bayyana cewa rashin lafiyarsa ta ci gaba da kamari ne bayan wasu daga cikin abokansa makusanta sun rasu cikin kwanakin nan.
Hashim farfesa ne mai murabus a fannin kimiyyar siyasa kuma marubuci ne. Ya fara aiki a shekarar 1948 kuma ya kai matsayin babban sakataren gwamnati kafin ya yi murabus a 1979. Bayan ya yi murabus, ya koma jami'ar Bayero da ke Kano inda ya koyar na shekaru masu yawa. Ana ci gaba da samun mace-mace a jihar Kano amma na karshe shine na Farfesa Hashim.
A kalla bincike kashi biyu masu zaman kansu aka gudanar a birnin Kano a kan yawan mace-macen nan. A wata hira da aka yi da Nasir Gwarzo a BBC Hausa, ya ce kungiyarsa ta zargi alaka mai karfi tsakanin mace-macen da ake yi da cutar coronavirus. Ya ce annobar ta wuce matakai biyu na farko a birnin, yanzu ta kai ga mataki na uku kuma mafi muni da tsoro. Kwamitin fadar shugaban kasa kasa a kan yaki da cutar coronavirus ta sanar da cewa jami'ai 3,000 aka tura jihar Kano don tallafawa wajen yaki da cutar.
A ranar Juma'a, Gwamna Abdullahi Ganduje ya sanar da kyautar dakin gwaji na tafi-da-gidanka da shahararren dan kasuwa Aliko Dangote ya yi wa jihar. Wasu ma'aikatan lafiya a jihar Kano sun zargi halin da jihar ke ciki da halin ko-in-kula da jama'ar jihar ke nunawa a bangaren bin dokar hana yaduwar cutar.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP
0 Response to "Mace-macen Kano: Allah ya yi wa tsohon Jarman Kano rasuwa"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?