
Korona ta sake hallaka mutane biyu a Kaduna
Sunday, 10 May 2020
Comment
ROHOTON: https://hausa.legit.ng/
Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da mutuwar karin wasu mutane biyu da ke jinyar cutar korona, lamarin da ya mayar da adadin mutanen da suka mutu saboda annobar a jihar zuwa mutane uku.
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya ce sabbin mutanen biyu da suka mutu sune; wani babban mutum daga karamar hukumar Makarfi da kuma wata mata daga Zaria.
A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na tuwita, gwamnan ya ce an sake samun karin mutane biyu da suka kamu da kwayar cutar, lamarin da ya mayar da adadin masu korona a jihar zuwa mutane 87.
A cewar gwamnan, mutane biyun da suka kamu da kwayar cutar sun hada da wani namiji daga karamar hukumar Igabi da wata mace daga karamar hukumar Chikun.
KADUNA UPDATE: Two more persons have tested positive, a male from Igabi and a female from Chikun. Two fatalities have also been recorded: a senior citizen from Makarfi and a lady from Zaria.— Governor Kaduna (@GovKaduna) May 9, 2020
Kaduna State now has 87 active Covid-19 cases and three fatalities.
A ranar 2 ga watan Mayu aka fara samun mutum na farko da cutar korona ta kashe a jihar Kaduna. Marigayin, tsohon ma'aikacin gwamnati ne, da ya boye gaskiyar cewa ya yi bulaguro zuwa Kano. Ya mutu ne kafin sakamakon gwajinsa ya fito.
> KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Korona ta sake hallaka mutane biyu a Kaduna"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?