
Kisan Khashoggi: Mun yafe wa waɗanda suka kashe mahaifinmu_Salah Khashoggi
Friday, 22 May 2020
Comment
![]() |
MARGAYI JAMAL KASHOGGI |
'Ya'yan marigayi Jamal Khashoggi, dan jaridar nan dan kasar Saudiyya da aka yi wa kisan gilla, sun ce sun yafe wa wadanda suka kashe mahaifinsu.
Dan marigayin mai suna Salah Khashoggi ne ya wallafa wannan sakon a shafinsa na Twitter da sanyin safiyar yau Asabar.
— salah khashoggi (@salahkhashoggi) May 21, 2020
SALAH KASHOGGI
Sakon da Salah Khashoggi ya wallafa a Twitter na cewa: "A wannan dare mai albarka na wannan wata mai tsarki, muna tunawa da abin da Allah Madaukakai Ya ce a Littafinsa mai tsarki: Ramuwa na mummunan aiki da irinsa tamkar an biya mummunan aiki da wani mummunan aikin ne. Amma duk wanda ya yafe kuma yayi sulhu, to ladansa na tare da Allah. Allah ba Ya son azzalumi."
A cikin sakon, Salah ya ci gaba da cewa: "Saboda haka mu 'ya'ya maza na shahidi Jamal Khashoggi, muna sanar da cewa mun yafe wa wadanda suka kashe mahaifinmu - Allah Ya jikansa - fi sabil lilahi, kuma muna neman dacewa da lada daga Madaukakin Sarki."
A dai kashe Khashoggi ne a watan Oktoban 2018 yayin wata ziyara da ya kai ofishin jakadancin Saudiyya da ke Santanbul na kasar Turkiyya.
A watan Disambar 2019, an yanke wa wasu mutum biyar hukuncin kisa, bayan wasu mutum uku da aka yanke wa hukuncin daurin mai tsawo saboda hannun da suke da shi a kisan gillar.
Mutum ukun da aka daure na tsawon shekara 24 ne saboda samunsu da aka yi da "hannu wajen boye kisan da kuma karya doka da suka yi."
Amma Shalaan Al Shalaan, wanda shi ne mataimakin mai shigar da kara kuma kakakin ma'aikatar shari'ar Saudiyya ya ce binciken da suka gudanar ya nuna cewa gabanin kisan, "babu wata kiyayya tsakanin" wadanda aka yankewa hukuncin kisan marigayin da shi kansa Jamal Khashoggin.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Kisan Khashoggi: Mun yafe wa waɗanda suka kashe mahaifinmu_Salah Khashoggi"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?