--
Kisan George Floyd baqar fata: Tarzoma ta barke a biranen Amurka

Kisan George Floyd baqar fata: Tarzoma ta barke a biranen Amurka



Yadda ake gumurzu tsakanin 'ya sanda da masu zanga-zanga a birnin Atlanta na jihar Georgia
An ba da umarnin kafa dokar hana fita a biranen Amurka a wani yunƙuri na kawo karshen tashe-tashen hankula tsakanin masu zanga-zanga da 'yan sanda dangane da mutuwar George Floyd.

Zanga-zangar da ake yi, tsakanin 'yan sanda da masu tayar da kayar baya ya sa 'yan sanda suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye da harsasai bayan an rika kai musu hare-hare a birane da dama.

Shugaba Trump ya zargi 'yan wawa da masu ra'ayin zaman kara-zube da masu matsanancin tsattsauran ra'ayi da wannan hargitsi, mafi muni tun bayan hawansa karagar mulki.

Mista Floyd ya rika maimaita wa 'yan sanda cewa ba ya iya numfashi, amma ba su kyale shi ba.


An kashe Mista Floyd, wani Ba'amurke mai shekara 46, a lokacin da yake hannun 'yan sanda a Minneapolis ranar Litinin.

Kuma an tuhumi dan sanda Derek Chauvin, mai shekara 44, da laifin kisan, kuma ana saran zai gurfana gaban kotu ranar Litinin.

A cikin hotunan bidiyo da ake yadawa ta yanar gizo, ana iya ganin Mista Chauvin ya durƙusa da gwuiwoyinsa kan wuyan Mista Floyd har na wasu mintoci, duk da Mista Floyd ya rika maimaita cewa ba ya iya numfashi.

Menene sabo game da zanga-zangar?
Manyan zanga-zangar sun bazu zuwa a kalla birane 30 a fadin Amurka.

A birnin Chicago, masu zanga-zangar sun rika jifar jami'an tsaro, wadanda suka mayar da martani ta hanyar harba hayaki mai sa hawaye. An kama mutane da yawa a ranar Asabar.

'Yan sanda a Los Angeles sun harba harsasai na roba a yayin da suke kokarin tarwatsa taron da masu zanga-zangar suka rika jefa kwalabe kan motocin 'yan sandan. Daga baya hotunan bidiyo sun nuna masu zanga-zangan tsaye kan motocin 'yan sandan da suka lalata.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Kisan George Floyd baqar fata: Tarzoma ta barke a biranen Amurka"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?