--
Katsina: Shahararrun 'yan bindiga 6 sun shiga hannun jami'an tsaro, an kashe wasu 2

Katsina: Shahararrun 'yan bindiga 6 sun shiga hannun jami'an tsaro, an kashe wasu 2

ROHOTON: LEGIT.NG

Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta damke wasu gagararrun 'yan bindiga shida da suka addabi karamar hukumar Dutsinma ta jihar. An samu shanu 130 tare da tumaki 225 a tare da 'yan bindigar. Biyu daga cikin 'yan bindigar 'yan asalin kauyen Shamushalle,

wasu biyun daga kauyen Nahuta da ke karamar hukumar Batsari sai sauran biyu daga kananan hukumomin Kurfi da Safana ta jihar. A wata takarda da jami'in hulda da jama'a na 'yan sandan jihar, SP Gambo Isah yasa hannu, ya ce an kama 'yan bindigar ne a ranar Laraba wurin karfe 10 na dare.

Jami'an sun bibiyi rahoton sirrin da suka samu ne bayan sanar dasu da aka yi cewa 'yan bindigar sun tsere zuwa dajin Rugu sakamakon tsananta ruwan wutar da dakarun sojin Najeriya suka yi a yankin. A halin yanzu, rundunar hadin guiwa da suka hada da 'yan sanda tare da tubabbun 'yan bindigar ne suka samu jagoranci daga Sani Muheddinge, sun kashe masu garkuwa da mutane biyu.

Samamen da suka kai ranar Laraba ya yi sanadain ceto mutum uku daga hannun masu garkuwa da mutanen tare da samun bindiga daya kirar AK 47. A wani labarin na daban, mun ji cewa an yi garkuwa da shugaban kungiyar kiristoci na jihar Nasarawa (CAN), Bishop Joseph Masin. Tsohon sakataren kungiyar kiristocin ta kasa,

Yohanna Samari ne ya tabbatar da aukuwar lamarin a garin Lafia. Ya ce wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba ne suka tsinkayi gidan shugaban kungiyar a cikin dare. Gidansa na yankin Bukan Sidi da ke garin Lafia, babban birnin jihar Nasarawa. Tuni suka yi awon gaba da shi zuwa wani wuri da har yanzu ba a sani ba, jaridar Daily Trust ta ruwaito. Kwamishinan 'yan sandan jihar, Bola Longe ne ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Ya ce masu garkuwa da mutanen sun yi gaba da shugaban CAN din ne a kan babura. Longe ya kara da cewa jami'an 'yan sanda na kokarin bankado inda masu garkuwa da mutanen suke don ceto rayuwan shugaban ba tare da wani hatsari ba.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/



KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Katsina: Shahararrun 'yan bindiga 6 sun shiga hannun jami'an tsaro, an kashe wasu 2 "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?