--
Jigawa: Yadda 'yan bindiga suka bi ɗan kasuwa har gadon jinyarsa suka sace shi

Jigawa: Yadda 'yan bindiga suka bi ɗan kasuwa har gadon jinyarsa suka sace shi



ROHOTON: LEGIT.NG

'Yan bindiga a ranar Asabar sun sace dan kasuwa, Yusuf Maifata a gidansa da ke garin Sankara da ke karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa. Mazauna unguwar sun ce yan bindigan sun isa unguwar ne misalin karfe 1.47 na dare dauke da bindigu suna harbe harbe wadda hakan ya sa mutane suka firgita sannan suka sace Maifata daga gidansa.

Wani daga cikin iyalan dan kasuwar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, "Maifata ya dade yana fama da rashin lafiya. An sallamo shi daga asibiti ranar Alhamis yana murmurewa a gida ne sai kwatsam abin ya faru."

Majiyar ya kuma bayyana cewa yan bindigan sun kira iyalansa sun nemi a biya su Naira miliyan 40 a matsayin kudin fansa. Sun kuma tambayi irin abincin da dan kasuwan ya saba ci da magungunan da asibiti suka rubuta masa ya rika sha. Yana sume suka tafi da shi saboda firgicin karar harbin bindiga da ya rika ji yayin da ya ke kwance a gadonsa kafin su shiga gidan su dauke shi kamar yadda majiyar ya ce shaidawa Premium Times.

 Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Jigawa, Audu Jinjiri ya tabbatar da afkuwar lamarin. Mr Jinjiri ya ce tuni rundunar ta baza jamianta na sashin yaki da masu fashi da makami da garkuwa da mutane su bi sahun yan bindigan domin ceto dan kasuwan mai shekaru 75 da haihuwa.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657


0 Response to "Jigawa: Yadda 'yan bindiga suka bi ɗan kasuwa har gadon jinyarsa suka sace shi "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?