
Gwamnatin jiha ta bayyana cututtuka biyu da ke kashe mutane a Kano
Saturday, 2 May 2020
Comment
Mai magana da yawun gwamna Ganduje, Salihu Yakasai ya cewa galibin wadanda suka mutu ba su samu kulawan likitoci ba kafin suka mutu. Gwamnatin jihar tare da hadin gwiwa da Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, da Hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta Afirka da ta Najeriya, NDCD, suna bincike don gano abinda ya yi sanadin mace macen da wasu ke dangantawa da COVID-19.
Mista Yakasai ya shaidawa gidan rediyon DW Hausa a ranar Jumaa cewa majinyatan da ke fama da wasu cututtukan "sun mutu ne don ba su samu kulawa daga asibitocin gwamnati da masu zaman kansu ba a lokacin ana fargabar COVID-19." Ya kuma ce mafi yawancin asibitoci masu zaman kansu a jihar ba su aiki saboda annobar ta korona. Akwai yiwuwar wannan ya shima yana daga cikin dalilan da yasa aka samu mace macen da yawa a jihar.
Ya ce gwamnan jihar ya gana da masu asibitoci masu zaman kansu a kan batun. Ya kuma bayyana cewa mambobi hudu na kwamitin kar ta kwana na yaki da COVID-19 a jihar sun kamu da coronavirus. Amma ya nuna rashin jin dadinsa yadda wasu mutane ke izgili game da lamarin da ya ce hakan na iya kawo koma baya cikin yaki da cutar da ake yi a jihar. Ya ce ma'aikatan lafiya suna bukatar yabo ne da goyon baya ba cin mutunci ba.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP
0 Response to "Gwamnatin jiha ta bayyana cututtuka biyu da ke kashe mutane a Kano "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?