
Da duminsa: An samu sabbin masu korona 386 a Najeriya, jimillar ta kusa 4,000
Friday, 8 May 2020
Comment
Hukumar kula da cututtuka masu yaduwa (NCDC) ta tabbatar da cewa, an samu sabbin masu dauke da cutar korona 386 a Najeriya a ranar Juma'a, 8 ga watan Mayun 2020. Kamar yadda hukumar ta bayyana, jihar Legas ce a kan gaba inda take da sabbin masu cutar har 176.
Jihar Kano ce ke biye da jihar Legas inda ta ke da sabbin masu cutar 65. A jihar Katsina an samu sabbin kamun cutar har mutum 31. Babban birnin tarayya na da 20, jihar Borno na da 17, jihar Bauchi na 15, jihar Nasarawa na da 14, jihar Ogun na da 13, jihar Filato na da 10 sai jihar Oyo na da 4,
Kamar yadda hukumar ta wallafa a shafinta na twitter, a jihar Sokoto an samu mutum 4, jihar Ribas akwai sabbin mutum 4, jihar Kaduna na da sabbin masu dauke da cutar 3 sai Edo da ke da 2. Jihar Ebonyi na da karin mutum 2, Ondo na da karin 2 sai jihohin Enugu, Imo, Gombe da Osun da ke da daddaya.
A halin yanzu jimillar wadanda suka kamu da cutar a Najeriya sun kai 3,912. An sallama majinyata 679 bayan an tabbatar da samun warakarsu daga muguwar cutar. Mutum 117 suka riga mu gidan gaskiya bayan kamuwa da cutar.
386 new cases of #COVID19;— NCDC (@NCDCgov) May 8, 2020
176-Lagos
65-Kano
31-Katsina
20-FCT
17-Borno
15-Bauchi
14-Nasarawa
13-Ogun
10-Plateau
4-Oyo
4-Sokoto
4-Rivers
3-Kaduna
2-Edo
2-Ebonyi
2-Ondo
1-Enugu
1-Imo
1-Gombe
1-Osun
3912 cases of #COVID19 in Nigeria
Discharged: 679
Deaths: 117 pic.twitter.com/IUWL9ROjqQ
A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta'aziyyarsa ga danginsa da kuma jama'ar garin Daura bayan rasuwar dan shi na dangi, Alhaji Murtala Dauda. Alhaji Murtala Dauda kani ne ga Malam Mamman Daura,
babban shakiki kuma aminin shugaban kasa Muhammadu Buhari. A wata takarda da ta fita daga hannun babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, Garba Shehu ya ce mutuwa rigar kowa ce kuma kowa sai ya dandanata.
Ya ce, "A madadina da na iyalaina, ina mika sakon ta'aziyyata a kan rashin Muntari Dauda. "Mutuwa na kan kowa kuma babu mai guje mata. Kowacce rai za ta dandana mutuwa wata rana. "Ba kukanmu mamatanmu ke so ba saboda hawayenmu ba zai dawo da su ba. Abinda suke bukata shine addu'a. "A don haka nake ta'aziyya ga jama'ar garin Daura gaba daya a kan wannan babban rashi."
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
- KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI:
0 Response to "Da duminsa: An samu sabbin masu korona 386 a Najeriya, jimillar ta kusa 4,000"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?