
COVID-19: SEMA ta bayyana yawan jama'ar da za su samu tallafi a jihar Kano
Friday, 1 May 2020
Comment
Sakataren hukumar al'amuran gaggawa na jihar Kano, SEMA, Dr Saleh Jili ne ya sanar da hakan yayin duba hatsin da gwamnatin tarayya ta bai wa jihar Kano. Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta tura motoci 110 na hatsi don a raba wa mabukatan jihar Kano don rage radadin kullesu da aka yi.
Jili yace gwamnatin jihar tana fatan gidaje 300,000 ne tallafin zai kaiwa a jihar. Ya kara da cewa, kusan mutum miliyan daya ne ake tsammanin za su mora daga wannan tallafin. Sakataren SEMA ya jinjinawa gwamnatin tarayya da irin kyautatawar da tayi. Ya kara da cewa hakan zai taka rawar gani wurin taimakawa marasa karfi a jihar.
Ya sake jaddada kokarin gwamnatin jihar wajen adalci a raba kayan tallafin ga mabukata. Hakazalika, Sanusi Ado, shugaban NEMA, ya ce akwai motocin hatsi har 25 da za su shiga jihar Kano din a ranar Alhamis. Ado ya ce za a adana hatsin a wurare biyar na jihar don a samu sauki rabonsu ga mabukata. Ya ce tallafin na daga cikin umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari na raba kayan rage radadi ta hannun ma'aikatar noma da kiwo da kuma habaka karkara.
Ado ya ce motocin hatsin za su kammala isowa ne a kwanaki kalilan masu zuwa. Hatsin sun hada da dawa, gero, shinkafa da masara. "An fitar da hatsin daga ma'adanar abincin kasar nan da ke Dutsinma a jihar Katsina, Lafia a jihar Nasarawa, Minna a jihar Niger, Gusau a jihar Zamfara da kuma Yola a jihar Adamawa," yace.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP
0 Response to "COVID-19: SEMA ta bayyana yawan jama'ar da za su samu tallafi a jihar Kano "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?