--
Covid-19: Sabbin mutane 220 sun kamu, 11 sun mutu a Borno, ta lafa a Kano

Covid-19: Sabbin mutane 220 sun kamu, 11 sun mutu a Borno, ta lafa a Kano



A cikin NCDC ta saba fitarwa kusan 12:00 na daren kowacce rana a shafinta na tuwita, ta sanar da cewa karin sabbin mutane 220 ne aka tabbatar da cewa kwayar cutar covid-19 ta harba a fadin Najeriya. Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11:56 na daren ranar Asabar, 02 ga watan Mayu, 2020. NCDC ta fitar da jerin jihohi da jimillar ma su dauke da kwayar cutar a kowacce jiha kamar haka;

62-Lagos 52-FCT 31-Kaduna 13-Sokoto 10-Kebbi 9-Yobe 6-Borno 5-Edo 5-Bauchi 4-Gombe 4-Enugu 4-Oyo 3-Zamfara 2-Nasarawa 2-Osun 2-Ebonyi 2-Kwara 2-Kano 2-Plateau R




 NCDC ta ce ya zuwa karfe 11:50 na daren ranar Asabar, 02 ga watan Mayu, akwai jimillar mutane 2388 da aka tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar covid-19 a Najeriya. An sallami mutane 385 bayan an tabbatar da samun saukinsu, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 85.

An samu jimillar mutane 69 da aka tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar covid-19 a jihar Borno. Daga cikin jimillar mutane akwai ma'aikatan lafiya 16 da su ka kamu da kwayar cutar yayin aikin taimakon masu jinyarta a jihar Borno. Kazalika, annobar ta yi sanadiyyar mutuwa mutane 11 a jihar Borno. Usman Umar kadafur, mataimakin gwamnan jihar Borno, sannan shugaban kwamitin kar ta kwana a kan annobar covid-19, ne ya sanar da hakan ranar Asabar yayin da ya ke ganawa da 'yan jarida a Maiduguri.

Source: Legit.ng 




KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com




KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/



KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP

0 Response to "Covid-19: Sabbin mutane 220 sun kamu, 11 sun mutu a Borno, ta lafa a Kano "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?