
COVID-19: Mu na ji mu na gani ciwon hanji ya kashe Kaninmu - Bethamary Okey
Tuesday, 12 May 2020
Comment
Mawakiyar Najeriya, Bethamary Okey ta bada labarin yadda wani ‘danuwanta na jini mai suna Sylvester, ya rasu a sakamakon kin karbarsa da aka yi a wasu asibitoci a Legas. Jaridar Punch ta ce Bethamary Okey ta ce tsoron yiwuwar kamuwa da cutar COVID-19 ta sa asibitoci da-dama da ke cikin garin Legas su ka ki karbar jinyar wannan kanin na ta.
A cewar mawakiyar, marigayin ya na fama ne da ciwon hanji tun kafin barkewar annobar Coronavirus. A watan Afrilu wadanda su ke kula da shi su ka bukaci ya canza asibiti. Tauraruwar ta ce an bukaci su maida maras lafiyan zuwa asibitin koyon aikin jinya na jami’ar Legas da ke garin Idi-Araba, amma likitoci su ki bari a kwantar da shi a kan gadonsu.
Bayan haka ta ce sun garzaya asibitin koyon aiki na jami’ar Legas da ke garin Ikeja, a nan ma dai malaman asibitin sun ji tsoron cewa mara lafiyan ya na dauke da kwayar COVID-19.
“Abin da ya sa ‘danuwana ya sallama shi ne asibitoci sun ki bari a karbe sa har a duba sa. Saboda takaici ‘danuwana ya mutu da kimanin karfe 6am na safiyar ranar 5 ga watan Mayu.” Wani dareka na asibitin LASUTH, Ibrahim Mustafa ya musanya wannan batu, ya ce ba su korar marasa lafiya. Bayan haka likitan ya ce ba su tambayar sakamakon gwajin COVID-19. Dazu kun ji cewa ruwan wuta ya sa Abubakar Shekau ya fito ya na kuka a wani sabon faifai. Shugaban ‘yan ta’addan ya na neman tsari daga luguden da soji su ke yi Boko Haram.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "COVID-19: Mu na ji mu na gani ciwon hanji ya kashe Kaninmu - Bethamary Okey"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?