
COVID-19: Masu korona na barazanar komawa gida a Jihar Niger (Bidiyo)
Thursday, 7 May 2020
Comment
ROHOTON: https://hausa.legit.ng/news/
Wasu majinyatan cutar coronavirus da ke killace a cibiyar killacewa a garin Minna, jihar Neja sun yi barazanar sallamar kansu a kan yadda ake nuna musu halin-ko-in-kula.
A wani bidiyo da SaharaReporters ta gani a ranar Laraba, wasu daga cikin majinyatan sun nuna tsananin fushinsu a kan halin da suke ciki. Sun ce yadda ake ciyar dasu bai gamsar dasu ba.
A wani labarin na daban, dan majalisar jihar Yobe, Lawan Nguru ya kamu da cutar COVID-19, ya sanar da hakan a ranar Laraba. Dan majalisar ne ke wakiltar mazabar Nguru kuma shi kadai ne daga jam'iyyar adawa ta PDP a majalisar,
kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa. A wata takarda da ta fito daga dan majalisar a garin Damaturu, ya ce ya killace kansa kamar yadda masana kiwon lafiya suka sanar. Amma kuma, ya musanta rahoton cewa ya ki killace kansa. Ya jaddada cewa ba zai taba yin zagon kasa ga kokarin gwamnatin jihar na shawo kan annobar tare da saka rayukan jama'a a hatsari ba.
Ya bayyana tabbacin cewa yadda gwamnatin jihar Yobe ke daukar mataki a kan cutar, za a shawo kan annobar. Ya shawarci jama'ar jihar da su kiyaye shawarwarin masana kiwon lafiya wajen hana yaduwar cutar. Nguru ya ce: "A halin yanzu, ina cibiyar killacewa kuma ina samun saukin halin da nake ciki. Ina jiran umarnin likitoci.
"Ina sake jinjina ga gwamnatin jihar Yobe a kan yadda take kula da mu masu jinyar jihar da kuma kokarin hana yaduwar cutar."
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP
0 Response to "COVID-19: Masu korona na barazanar komawa gida a Jihar Niger (Bidiyo) "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?