--
Coronavirus a Najeriya: Yawan masu cutar ya zarce dubu goma

Coronavirus a Najeriya: Yawan masu cutar ya zarce dubu goma



Yawan masu cutar korona a Najeriya ya kai wani gagarumin mataki, inda ya zarce mutum 10,100.

Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ta ƙasar ta nuna cikin alƙaluman da fitar cewa an gano ƙarin mutum 307 ranar Lahadi da suka sake kamuwa da ƙwayar cutar.

Matakin na zuwa ne kwana guda bayan samun adadin masu korona mafi yawa cikin kwana guda, wato jimillar mutum 553, tun bayan ɓullar annobar Najeriya a ƙarshen watan Fabrairu.

A yau ma Legas, jihar da annobar ta fi tsanani a Najeriya, an sake samun mutum 188 da suka kamu.

Abuja kuma, babban birnin Najeriya, mutum 44 ne aka ba da rahoton cutar ta sake shafa. Yawan masu cutar yanzu a Abuja, 660.

Haka zalika, alƙaluman NCDC sun nuna cewa Allah Ya yi wa masu cutar korona 14 rasuwa a ranar ta Lahadi.

Sai dai kuma, an sallami masu cutar 151 daga cibiyoyin killacewa cikin sa'a 24 da ta wuce,bayan an tabbatar da warkewarsu.

Jihar Ogun, ta sake samun mutum 19 da korona ta shafa. Sai Kaduna, inda aka gano mutum 14. Duka-duka akwai masu korona 258 a Kaduna.

Oyo, jiha ta biyu mafi yawan masu cutar a yankin kudu maso yammacin Najeriya, mutum 12 sun sake kamuwa. A Bayelsa an sake gano mutum tara.

A Gombe, mutanen da ke fama da cutar, sun ƙaru da mutum biyar ranar Lahadi. Kano kuma mutum uku. Ƙwararru dai sun fara tambayar shi me ke faruwa, alƙaluman masu cutar ya ja baya a jihar.

Mutum uku sun sake kamu da cutar a jihar Delta. Jihohin Imo da Rivers da Neja da kuma Bauchi duk an sake gano masu cutar bi-biyu.


Muhimman bayanai kan annobar korona

A wani abu da ba a taɓa gani ba tun bayan ɓullar annobar korona a Najeriya, hukumomin ƙasar ranar Asabar 30 ga watan Mayu, sun ba da rahoton gano mutum 553 da cutar ta sake harba.

An fara gano cutar korona a Najeriya ne a jikin wani baturen kasar Italiya ranar 27 ga watan Fabrairu bayan ya shiga kasar ta filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas.

Shi da mutum na farko da ya kamu da cutar ranar 20 ga watan Maris a arewacin Najeriya, Mohammed Atiku duk sun warke kuma an sallame su daga asibiti.

A ranar Juma'a 17 ga watan Afrilu ne cutar korona ta yi sanadin mutuwar Malam Abba Kyari, shugaban ma'aikatan fadar shugaban Najeriya. Shi ne mutum mafi girman mukami da ya mutu dalilin korona a kasar.

Gwamnoni irinsu Bala Mohammed da Nasir El-rufa'i da kuma Seyi Makinde na jihar Oyo duk sun kamu da annobar kafin su warke daga bisani.

Bayan kimanin wata uku da ɓullar cutar a Najeriya, karon farko hukumomi a ranar Laraba 27 ga watan Mayu sun ce mutum biyu sun kamu da korona a jihar Kogi.

Wasu sun yi ta zargin cewa annobar ta daɗe ta shiga jihar, rashin yin gwaji ne ya sa aka shafe tsawon lokaci kafin a iya tabbatar da ita.

Jiha ɗaya ce a hukumance har yanzu ba a samu ɓullar korona cikinta ba a Najeriya. Ko da yake, ita ma wasu na cewa mai yiwuwa ne akwai annobar a jihar ta Cross river, amma gwaji ne zai tabbatar da gaskiya.

Hukumomin Najeriya dai sun ce sun rubanya yawan gwaje-gwajen da suke yi a kasar, inda a yanzu suka ce akan yi gwaji kimanin dubu guda cikin sa'a 24.

Ga jerin bayanan jihohin da korona ta bulla cikinsu ya zuwa daren Lahadi 31 ga watan Mayu.



 KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Coronavirus a Najeriya: Yawan masu cutar ya zarce dubu goma"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?