An kwashe makonni cikin dokar hana fita a wadannan jihohin domin dakile yaduwar cutar korona a kasar. Kasuwannin Legas sun cika da mutane, mafi yawa kuma ba su sanya takunkumi ba, a ranar Litinin 4 ga watan Mayu 2020
Wasu 'yan kasuwa a jihar Legas suna sauka daga motar hayar da suka hau zuwa inda suke kasuwanci Masu hawa mota a bakin wajen hawa mota a jihar Legas, a ranar Litinin 5 ga watan Mayu 2020
Duk da cewa akwai bukatar a rika ba da tazara tsakanin mutane, amma da yawa basu damu da wannan dokar ba saboda damuwar da ake ciki.
Kasuwar Kwari a Jihar Kano bayan sassauta dokar kulle ta mako biyu da gwamnatin tarayyar kasar ta kakaba a jihar, an dauki hoton a ranar Litinin 4 ga watan Mayun 2020 Cunkoson motoci a Abuja a safiyar ranar Litinin 4 ga watan Mayu 2020
Wani mai zuba mai a daya daga cikin gidajen mai a Abuja, bayan janye dokar hana fita da aka janye a birnin Wasu daga cikin 'yan kasuwa a Abuja da ke kokarin shiga kasuwannin a ranar Litinin 4 ga watan Mayu 2020
Kasuwar Wuse daya daga cikin manyan kasuwanni a Abuja, za a rika bude kasuwannin Abuja a ranakun Laraba da Asabar Wani mai tallan Mangwaro a Abuja a ranar litinin 4 ga watan Mayu 2020, sanye da takunkumin fuska
Wani dan sanda a Abuja sanye da takunkumi a ranar Litinin 4 ga watan Mayu 2020 Kasuwar ta ciki da mutane sai dai al'umma na kukan babu abin da za su iya siyayyar da su
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "Coronavirs: Hotunan yadda aka bude jihohin Lagos da Kano da Kuma Abuja"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?