--
Akwai lauje cikin nadi: Trump ya ce ba zai kara sanya takunkumi ba

Akwai lauje cikin nadi: Trump ya ce ba zai kara sanya takunkumi ba

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya isa kamfanin mota na Ford dake Michigan a ranar Alhamis da takunkumi na fadar shugaban kasar Amurka mai dauke da tambarin kasar, amma yaki ya sanya takunkumin a lokacin da zai yi magana da manema labarai.

“Ba zan bawa manema labarai damar ganinshi ba,” cewar Trump kafin ya cire takunkumin daga fuskar shi, wanda yace yana sanye dashi kafin ya cire lokacin hira da manema labaran. “Yana da matukar kyau, amma sun ce ba dole bane.”

Wannan wani misali ne da shugaban kasar ya sake karyawa a yayin da hukumomi suke kokarin ganin kowa yabi domin dakile cutar Coronavirus.

Trump dai ya shiga wannan masa’anta ta Ford babu komai a fuskarshi, inda manyan shugabannin kamfanin suka zagaye shi kowanne sanye da takunkumi a fuskarshi. Doka ce a wannan masana’anta mutum ya shiga ba tare da takunkumi ba.

‘Ya rage na shi,” cewar Bill Ford. shugaban kamfanin a lokacin da aka yi masa tambayar mai yasa Trump baya bin dokar kamfanin. Daga baya mai magana da yawun kamfanin na Ford, Henry Ford, ya bukaci shugaba Donald Trump da ya sanya takunkumi a lokacin da ya iso.

Ya sanya takunkumin a lokacin ganawar sirri da aka yi da shi a kamfanin a cikin wannan shekarar,” cewar kamfanin. “Daga baya shugaban kasar ya cire takunkumin.”

A rahoton da CNN ta kawo, Trump ya bukaci jihohi da su cire dokokin da suka sanya akan al’umma na hana kasuwanci, sanya dokar zama a gida da kuma matsalar tattalin arziki da ake fama da ita.

“Dokar hana fita ba ita ce mafita ba a gare mu,” Trump ya ce. “Don kare lafiyar al’umma muna bukatar ingantaccen tattalin arziki.”


“Duk dan Amurka da yaga yana sha’awar komawa ya cigaba da aiki kamata yayi a goya masa baya ba a hana shi ba,” cewar shugaban kasar.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/



KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Akwai lauje cikin nadi: Trump ya ce ba zai kara sanya takunkumi ba"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?