
Adadin mutanen da aka tabbatar sun harbu da cutar korona a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun kai 666
Monday, 11 May 2020
Comment
Rohoton:https://www.bbc.com/hausa
Adadin mutanen da aka tabbatar sun harbu da cutar korona a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun kai 666, a cewar ma'aikatar lafiya ta jihar.
Wannan ya biyo bayan samun ƙarin mutum 64 da aka yi a ranar Litinin.
Kazalika ta ce ƙarin wasu shida sun rasa rayukansu sakamakon cutar, abin da ya kawo jumillar adadinsu zuwa 32.
Har wa yau, ƙarin mutum 13 sun warke daga cutar kuma an sallame su - jumillar adadinsu 63.
Jadawalin jihohin da cutar ta bulla da hukumar dakile cutuka masu yaduwa a Najeriya, NCDC ta fitar a daren Litinin ya nuna Kano ce ta biyu a yawan masu fama da cutar bayan Legas mai mutum 1,933.#COVID19KN Update as at 11:45pm 11th May 2020— Kano State Ministry of Health (@KNSMOH) May 11, 2020
*️⃣ 64 new cases of #COVID19Kano cases confirmed.
*️⃣ Total confirmed cases in @KanostateNg are now 666.
*️⃣ 13 additional #COVID19Kano patients were discharged.
*️⃣ 6 #COVID19Kano deaths were recorded.#MaskUpKano #PrayForKano pic.twitter.com/pcKFjRLtmY
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kafa dokar saka takunkumi tare da kafa kotuna na musamman domin hukunta wadanda aka kama ba tare da takunkumin ba.
Jihar ta kuma tsawaita dokar kulle da mako guda nan gaba a kokarin da take na shawo kan annobar.
A ranar 11 ga watan Afrilu ne hukumomi a Kano suka sanar da samun mutum na farko da ya kamu da cutar kuma tun daga wannan lokacin aka rika samun karuwar mutanen da annobar ta shafa.
Jihohi makwabtan Kano ma na ci gaba da fama - Katsina na da mutum 205, Jigawa na da 118, Bauchi na da 182, Kaduna na da 111.
Ya zuwa daren Litinin 11 ga watan Mayu, mutum 4,641 ne suka harbu da cutar korona a Najeriya, yayin da 150 suka rasu da kuma 902 da suka warke kuma aka sallame su.
242 new cases of #COVID19;— NCDC (@NCDCgov) May 11, 2020
88-Lagos
64-Kano
49-Katsina
13-Kaduna
9-Ogun
6-Gombe
4-Adamawa
3-FCT
1-Ondo
1-Oyo
1–Rivers
1-Zamfara
1-Borno
1-Bauchi
4641 cases of #COVID19 in Nigeria
Discharged: 902
Deaths: 150 pic.twitter.com/2eK1cRJeH0
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Adadin mutanen da aka tabbatar sun harbu da cutar korona a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun kai 666"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?