Abdullahi Gadon-Kaya ya bada shawarar yadda za a bude Masallatai a Ranakun Juma’a |vedio
Wednesday, 6 May 2020
Comment
- Abdullahi Umar Gadon Kaya ya na so a bar Jama’a su rika yin sallar Juma’a - Malamin ya ce idan za a iya fita kasuwa, za a iya kyale Musulmai su yi sallah - Sheikh Gadon Kaya ya ce akwai hanyar da za a bi wajen takaita sallar Juma’a Ganin halin da aka shiga na zaman kulle na makonni wanda har ta kai ba a iya fita sallar jami’i a jihohin Najeriya da-dama, malamai sun fara fitowa su na neman a ba su damar yin ibada.
Sheikh Abdullahi Umar Gadon-Kaya ya roki gwamnatocin da su bude masallatai domin a koma sallar Juma’a. Malamin ya roki a ba su dama daga cikin kwanakin da ake badawa a fita. Abdullahi Umar Gadon-Kaya ya yi wannan roko ne da babbar murya wajen wani karatu da ya yi a garin Kano. Shehin ya na ganin idan an hallata zirga-zirga, za a iya kyale sallar mutane.
Sheikh Gadon-Kaya ya ke cewa sai a kafa dokoki da sharudan da za a bi wajen yin sallar jami'in. A cewarsa za a iya amfani da ‘yan agaji wajen ganin kowa ya rufe fuskarsa a masallaci. Bayan rufe fuska da tsummar kariya, malamin addinin ya ke cewa za a iya hana kowa shiga cikin masallaci har sai daf da lokacin da za a fara hudubar juma’a, domin a kare lafiyar al’umma.
Gadon-Kaya ya ce limamai za su iya takaita huduba ta yadda za a yi sallah, a idar a cikin minti 20 zuwa 30. Shehin ya ce limamai sun sa hanyar da za su bi domin ayi maza a bada sallah. Malamin ya ce za a iya bada tazara a cikin masallatai ta yadda ba za a samu cakuduwar masu ibada ba. Ya ce abin na yi masa takaici ganin yadda aka dade ba a iya yin sallar juma’a ba. Tun da ana samun ranakun yin zirga-zirga a kasuwanni da bankuna ayi cefanen kayan amfani da na abinci, babban malamin ya roki gwamnati ta saki hanya a ranar Juma’a ayi sallah.
Wannan malami ya ke cewa wannan shawara da ya ke ba hukuma fahimtarsa ce, ya kuma nemi ayi masa kyakkyawan zato. A cewarsa sallar Juma’a tamkar larurar fita neman abinci ce. A wannan lokaci da ake fama da annobar COVID-19, Gadon-Kaya ya ce su na bin duk sharudan lafiya da dokokin da aka kafa, sai dai ya roki a ba musulmai wannan dama ta rana guda.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

This malam here have said it all nd i think we can make this happen please retweet till it reach the higher ups @MBuhari @BashirAhmaad @GovUmarGanduje please review this since its once a week then i think we can be fine, deploy police officers to make sure everything works well pic.twitter.com/v76PSOgABi— Lady luck 😍😍❤ (@_Ayusheer_) May 5, 2020
Gadon-Kaya ya ce limamai za su iya takaita huduba ta yadda za a yi sallah, a idar a cikin minti 20 zuwa 30. Shehin ya ce limamai sun sa hanyar da za su bi domin ayi maza a bada sallah. Malamin ya ce za a iya bada tazara a cikin masallatai ta yadda ba za a samu cakuduwar masu ibada ba. Ya ce abin na yi masa takaici ganin yadda aka dade ba a iya yin sallar juma’a ba. Tun da ana samun ranakun yin zirga-zirga a kasuwanni da bankuna ayi cefanen kayan amfani da na abinci, babban malamin ya roki gwamnati ta saki hanya a ranar Juma’a ayi sallah.
Wannan malami ya ke cewa wannan shawara da ya ke ba hukuma fahimtarsa ce, ya kuma nemi ayi masa kyakkyawan zato. A cewarsa sallar Juma’a tamkar larurar fita neman abinci ce. A wannan lokaci da ake fama da annobar COVID-19, Gadon-Kaya ya ce su na bin duk sharudan lafiya da dokokin da aka kafa, sai dai ya roki a ba musulmai wannan dama ta rana guda.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP
0 Response to "Abdullahi Gadon-Kaya ya bada shawarar yadda za a bude Masallatai a Ranakun Juma’a |vedio"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?