--
Za mu yi amfani da lambar BVN don binciko talakawa masu bukatar tallafi - Minista

Za mu yi amfani da lambar BVN don binciko talakawa masu bukatar tallafi - Minista




Gwamnatin tarayya ta ce za ta yi amfani da lambar tantance asusun banki (BVN), wajen gano talakawa da gajiyayyun 'yan Najeriya, domin basu tallafin rage radadi.



Ministar Jin dadi da Walwalar jama'a, Sadiya Farouq, ta bayyana hakan a jiya Talata, 21 ga watan Afrilu, a Abuja, a lokacin taron kwamitin fadar Shugaban kasa kan COVID-19.

Ta bayyana cewa ta wannan hanyar za a fi saurin yin rabon cikin sauki.
Ta ce, “Za mu yi amfani da wasu hanyoyi ciki harda lambar tantance asusun banki wato BVN. Za kuma mu yi amfani da layukan sadarwa wajen gano talakawa da gajiyayyu a kasar. Wannan zai fi sauri, zai kasance a bayyane sannan kuma zai fi sauki wajen lissafi.”


Ministar ta kara da cewa tsarin rabon kudi na hannu da hannu zuwa ga talakawa wanda ke gudana a yanzu a wasu yankunan kasar, yana tafiya ne bisa tsari kuma a bayyane.
A nashi bangaren, ministan labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammed, ya bayyana cewa gwamnati ta gabatar da sabbin hanyoyin wayar da kai domin hana yaduwar annobar COVID-19.

Ya bayyana cewa ma'aikatar ta fito da sabbin hanyoyin wayar da kai na gidajen talabijin da rediyo, domin isar da sakonni ga yan Najeriya kan yada za su kare kansu da kuma guje ma kamuwa da cutar.
Ya yi bayanin cewa an shirya wadannan kiraye-kirayen ne cikin harsunan Turanci, Hausa, Igbo da kuma Yarbanci, an kuma fara haskawa a tashar NTA da FRCN.

A gefe daya, mun ji cewa Bola Tinubu, ya bukaci gwamnatin tarayya (FG) ta yi amfani da lambar tantance asusun banki (BVN) wajen aika wa 'yan Najeriya kudin tallafin rage radadin matsin da annobar covid-19 ta haifar.
Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas, ya bayar da wannan shawara ne a cikin wani jawabi da ya fitar ranar Laraba a Legas.

Ya ce za a iya biyan kudi kai tsaye zuwa asusun wadanda za su ci moriyar tallafin ta hanyar amfani da BVN dinsu.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP

Related Posts

0 Response to "Za mu yi amfani da lambar BVN don binciko talakawa masu bukatar tallafi - Minista"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?