--
Za mu karbi Shekau da hannu biyu idan ya mika wuya — Rundunar Sojin Najeriya

Za mu karbi Shekau da hannu biyu idan ya mika wuya — Rundunar Sojin Najeriya



Rundunar Sojojin Najeriya ta ce za ta karbi shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau idan ya ajiye makamansa ya mika wuya kamar yadda Daily Trust ta ruwaito. Ta ce idan Shekau ya bi dokokin mika wuya yayin yaki ko tashin hankali, rundunar za ta karbe shi bisa tsarin irin wanda kasashen duniya suka amince a kai. Shugaban sashin watsa labarai na sojojin, Manjo Janar Enenche ne ya bayyana hakan a ranar Jumaa yayin hirar da ya yi da Channels TV.

Ya ce, "Kwararru sun yi nazarin bidiyon da Shekau ya fitar a baya bayan nan. Akwai rade radin cewa yana son ya mika wuya. "Idan har da gaske yan taadan za su mika wuya, akwai tsarin da ake bi don yin hakan. Idan Shekau ya bi wannan dokokin ya mika kansa, za mu amince da mika wuyansa."

A wani rahoton, mun kawo muku cewa Hedkwatan Tsaro ta Najeriya ta ce Dakarun Sojojin Saman ta karkashin Operation Lafiya Dole (OPLD), sun lalata wani gida da yan taaddan Boko Haram ke zaune a Bulawa kusa da dajin Sambisa a jihar Borno. Mai kula da sashin watsa labarai na hedkwatan tsaron, Manjo Janar John Enenche ne ya bayyana hakan cikin wata sako da ya fitar a shafin Twitter a ranar Alhamis a Abuja.

Enenche ya ce sojojin sun kai harin ne a ranar 21 ga watan Afrilu bayan samun bayanan sirri daga masu leken asiri da kuma amfani da naurar leken asiri ta zamani inda suka tabbatar yan taadan na gidan. Ya yi bayanin cewa an yi amfani da jiragen yaki da Rundunar Sojin Saman Najeriya inda suka yi ruwan bama bamai a gidan suka kashe yan taadan tare da lalata gidan. A cewarsa, an kashe wasu daga cikin yan taadan da ke zaune a gidan yayin harin.

Ya ce, "An murkushe wasu daga cikin yan Boko Haram din da su kayi yunkurin neman mafaka domin su kai wa jirgin yakin NAF hari bayan tarwatsa gidan. "Rundunar Sojojin Najeriya za ta cigaba da jajiracewa wurin aikin da ta sa a gaba na samar da zaman lafiya da tsaro a yankin Arewa maso Gabas da kare Najeriya daga makiyan ta."

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/


KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP

0 Response to "Za mu karbi Shekau da hannu biyu idan ya mika wuya — Rundunar Sojin Najeriya"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?