--
Yunkurin tserewar fursononi: Shugaban kurkukun Kaduna ya 'fede biri har bindi'

Yunkurin tserewar fursononi: Shugaban kurkukun Kaduna ya 'fede biri har bindi'

Sanusi Mu'azu Danmusa, shugaban hukumar gidajen gyaran hali na jihar Kaduna, ya kwatanta rahoton da wasu kafofin yada labarai ke yadawa da labarun kanzon-kurege, wadanda ba alamun gaskiya a cikinsu. Ya bayyana hakan ne a matsayin martanai a kan rahoton balle gidan gyaran hali na Kaduna da mazauna gidan suka yi yunkurin aikatawa

kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito. A wata takarda da ta fita a ranar Asabar, Danmusa ya ce tabbas wasu daga cikin mazauna gidan sun yi yunkurin balle gidan a ranar 31 ga watan Maris din shekarar 2020. Shugaban ya bayyana cewa tuni hukumar gidan ta yi bayani a kan aukuwar lamarin amma duk haka ta kara yanke shawarar kara bayani ne don mayar da martani a kan rade-radin da ke yawo a gari.

Shugaban gidajen gyaran hali na jihar Kaduna; SM Danmusa Source: Twitter 

Kamar yadda wani sashi na takardar ya bayyana, "Fitar wannan takardar na da matukar amfani. Muna tabbatarwa da jama'a cewa babu abinda hukumar ke son boyewa kamar yadda wasu sashi na kafafen yada labarai ke sanarwa.

"Ballantana an samu asarar rayuwa, mazauna gidan har hudu sun rasa rayukansu a asibiti sakamakon raunikan da suka samu. Hakan ta faru ne sakamakon yunkurin fashe gidan tare da tserewa da suka yi. Ya kara da cewa, "an fara gamsasshen bincike kamar yadda shugaban hukumar kula da gidajen gyaran hali na Najeriya, Alhaji Jafaru Ahmed, ya bada umarni."

KARANTA: Sautin murya: Shekau ya yi laushi a cikin sabon sakon da ya fitar don karfafawa mayakansa gwuiwa

DAGA MUJALLAR:https://www.bzglobalservice.com.ng/

LATSA NAN๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 





Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Yunkurin tserewar fursononi: Shugaban kurkukun Kaduna ya 'fede biri har bindi' "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?