
Yanzu-yanzu: Trump ya kira Buhari, ya yi alkawarin aiko da tallafi
Tuesday, 28 April 2020
Comment
- Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya kira shugaba Muhammadu Buhari a wayar tafi-da-gidanka a yau Talata - Kamar yadda ministan yada labarai, Lai Mohammed ya bayyana, Trump ya kira ne don jajantawa Buhari halin annobar da kasar nan ta shiga - Shugaban kasar Amurkan ya bayyana cewa zai aiko da na'urorin taimakon numfashi don amfanin asibitocin kasar nan Shugaban kasar Amurka,
Donald Trump ya kira shugaban kasa Muhammadu Buhari a waya a ranar Talata. Ya kira ne don jajantawa Najeriya halin da ta shiga na mummunar annobar Covid-19, jaridar The Cable ta wallafa. Kamar yadda Lai Mohammed, ministan yada labarai ya bayyana, shugaba Trump din ya dauka alkawarin aike wa Najeriya da sakon na'urorin taimakon numfashi.
Mohammed ya sanar da hakan ne a yayin jawabin kwamitin shugaban kasa na yakar annobar Covid-19. Kamar yadda Turmp ya yi alkawari, zai aiko da na'urorin taimakon numfashin ne don amfanin asibitocin Najeriya.
Yanzu-yanzu: Trump ya kira Buhari, ya yi alkawarin aiko da tallafi Source: UGC
Karin bayani na nan tafe...
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP
0 Response to "Yanzu-yanzu: Trump ya kira Buhari, ya yi alkawarin aiko da tallafi "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?