--
Yanzu-yanzu: Shugaban ma'aikatan fadar shugaban qasa Abba Kyari ya riga mu gidan gaskiya

Yanzu-yanzu: Shugaban ma'aikatan fadar shugaban qasa Abba Kyari ya riga mu gidan gaskiya



- Wata sanarwa da muke samu a yanzun nan ta bayyana cewa Allah ya yiwa shugaban ma'aikata Abba Kyari rasuwa - Babban makusancin ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rasu ne a jiya Juma'a 17 ga watan Maris bayan kamuwa da cutar Coronavirus

- Mai bawa shugaban kasa shawara a fannin sadarwa Mr Femi Adesina, shine ya bayyana haka a shafinsa na Twitter, inda yace za ayi jana'izarsa nan ba da dadewa ba Shugaban ma'aikatan shugaba Buhari, Abba Kyari ya riga mu gidan gaskiya, sanadiyyar kamuwa da cutar Coronavirus da yayi a cikin watan Maris. A jiya dai an bayyana rahoton cewa mutane 51 sun kamu da cutar ta Coronavirus a Najeriya, inda yawan masu cutar ya karu zuwa 493.

Yanzu-yanzu: Shugaban ma'aikatan fadar shugaban qasa Abba Kyari ya riga mu gidan gaskiya Source: Twitter 

Ya zuwa yanzu an yiwa mutane 159 magani, tuni har an sallamesu daga asibiti ma, inda mutane 17 suka mutu sanadiyyar kamuwa da cutar, kamar dai yadda cibiyar lura da manyan cututtuka ta Najeriya ta ruwaito.

Fadar shugaban kasar ta tabbatar da rasuwar tashi, bayan wani rahoto da mai bawa shugaban kasa shawara ta musamman a fannin sadarwa Mr Femi Adesina ya wallafa a shafinsa na Twitter.

"Fadar shugaban kasa za ta bayyana rasuwar shugaban ma'aikata na Najeriya, Malam Abba Kyari. Marigayin dai ya kamu da cutar ta Coronavirus, kuma yana karbar magani a asibiti, inda a jiya Juma'a 17 ga watan Afrilu Allah yayi masa rasuwa. "Allah ya yi masa rahama. Zamu bayyana yadda za'ayi jana'izarsa nan ba da dadewa ba,"

cewar Femi Adesina a sanarwar da ya wallafa. Labarin yadda ya kamu da cutar ta Coronavirus dai ya fito ne a watan Maris, inda bayan kamuwarshi da cutar, shi ma shugaban kasa Muhammadu Buhari aka yi masa gwaji ba a samu cutar a jikinshi ba. Shugaba Buhari, Yemi Osinbajo, gwamnoni da ministoci da dama sun hadu da shi kafin a gabatar da gwajin cutar a jikinshi. Kyari wanda ya dawo Najeriya daga wata tafiya da yayi zuwa kasar Jamus, a ranar 14 ga watan Maris,

ya gana da manyan mutane na Najeriya da dama. Abba Kyari daga baya ya fito ya bayyana cewa za a kai shi birnin Legas daga Abuja domin ya cigaba da karbar magani.KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/





LATSA NAN๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 






Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡
                            LATSA NAN DOMMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Yanzu-yanzu: Shugaban ma'aikatan fadar shugaban qasa Abba Kyari ya riga mu gidan gaskiya "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?