--
Yanzu-yanzu: An samu karin mutum daya mai Coronavirus a Kano ansaka dokar hana shige da fice

Yanzu-yanzu: An samu karin mutum daya mai Coronavirus a Kano ansaka dokar hana shige da fice



Maaikatar kiwon lafiyan jihar Kano ta bayyana cewa an samu karin mutum daya da suka kamu da cutar a jihar, kwana uku da bullar cutar a jihar. Hadimin gwamna Abdullahi Ganduje kan kafafen yada labarai, Salihu Tanko Yakassai, ya bayyana hakan ne da yammacin Talata, 14 ga Afrilu, 2020. A yanzu , adadin mutanen da ke dauke da cutar a Kano ya zama hudu.

Mun kawo muku ranar Asabar cewa mutumin farko da ya kamu da cutar a jihar Kano ya yi tafiya daga Legas zuwa Abuja sannan ya dira a Kano. An gwadashi ne a cibiyar gwajin dake asibitin koyarwan Aminu Kano AKTH. Tuni an garzaya da shi dakin killace mutane a Kwanar Dawaki. Bayan haka, Jami'an hukumar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC, sun shawarci tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya killace kansa bayan gwajin da akayi masa a jihar Kano.

Sakamakon bibiyan mutanen da mutumin farko da ya kamu cutar a Kano yayi mu'amala dasu, an gano cewa tsohon gwamna Lamido ya halarci wata jana'izar da mutumin ya halarta a Koki. Shugaban ma'aikatar kiwon lafiyan jihar Kano, Dr. Imam Wada Bello, ya tura wasikar kar ta kwana ga Sule Lamido inda ya bukaci daukar jini da yawunsa domin gwaji.

A wani labarin. Mai girma gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bada umarnin rufe jihar na mako daya. Dokar hana shige da fice a jihar Kano din za ta fara aiki ne daga ranar Alhamis, 16 ga watan Afirilun 2020. Kamar yadda mai bada shawara ta musamman ga gwamnan ya wallafa, ana sa ran dokar hana shige da ficen za ta yi aiki ne mako daya cif kafin a ga abinda hali yayi.

A tsawon lokacin, ba a bukatar kaiwa da kawowar jama'a ko ababen hawa a jihar. Gwamnan ya tabbatar da cewa jami'an tsaro za su damke duk wanda aka kama da laifin take dokar.KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/



LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 






Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇
                            LATSA NAN DOMMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

Related Posts

0 Response to "Yanzu-yanzu: An samu karin mutum daya mai Coronavirus a Kano ansaka dokar hana shige da fice"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?