
Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 19 yau a Najeriya, jimilla 362
Tuesday, 14 April 2020
Comment
An samu karin mutane ashirin (20) sun kamu da #COVID19; 14 aLagos 2 a Abuja 1 a Kano 1 a Akwa Ibom 1 a Edo “A karfe 9:20 na daren 14 ga Afrilu, mutane 362 suka kamu da COVID19 a Najeriya. 99 sun warke, kuma 11 sun mutu.“ “An tabbatar da bullar cutar a jihohi 19 a Najeriya.“
Ga jerin jihohi: Lagos- 203 FCT- 58 Osun- 20 Edo- 16 Oyo- 11 Ogun- 9 Bauchi- 6 Kaduna- 6 Akwa Ibom- 5 Katsina-5 Kwara- 4 Kano- 4 Ondo- 3 Delta- 3 Enugu- 2 Ekiti- 2
Rivers-2 Benue- 1 Niger- 1 Anambra- 1 A bangare guda, Ministan labarai, Lai Mohammed, ya ce gwamnatin tarayya ba zata iya raba wa yan Najeriya kudaden tallafi da hukumomi masu zaman kansu suka bayar don yakar cutar coronavirus ba.
A cewar NAN, ministan ya bayar da dalilan da yasa ba za a ba al’umman kasar kudin ba, a lokacin da ya bayyana a shirin “Politics Nationwide”, na Radio Nigeria a ranar Talata. Ya yi martani ne ga wata bukata da ke naman a raba wa yan Najeriya wani bangare na kudaden domin su toshe gibin da dokar hana fita ya yi masu. Ministan ya ce kudaden na inganta harkar lafiya ne, sannan cewa ba za a iya amfani dashi wajen samar da kayan rage radadi ba.
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇
LATSA NAN DOMMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE
KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 19 yau a Najeriya, jimilla 362 "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?