--
Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 16, Jimilla 305

Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 16, Jimilla 305

Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da cewa an samu karin mutane goma sha bakwai (17) da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya a ranar Jumaa, 10 ga Afrilu, 2020.

Cibiyar ta bayyana hakan a shafin ra'ayinta na Tuwita inda tace: “An tabbatar da mutane goma sha shida(16) sun kamu da #COVID19 a Najerya,

8 a Lagos
3 a Katsina
2 a Abuja
1 a Neja
1 a Kaduna
1 a Anambra
1 a Ondo

“Kawo karfe 9:30 na yammacin 10 ga Afrilu, mutane 305 aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Najeriya, an sallami mutane 58, kuma mutane 7 a rigamu gidan gaskiya.“


A yau, Juma'a, ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya gana da kwamitin 'ko ta kwana' da ya kafa a kan annobar cutar covid-19.

A cikin wata sanarwa da shugaba Buhari da kansa ya wallafa a shafinsa na Tuwita, ya bayyana cewa ya na matukar godiya ga kwamitin bisa jajircewarsa a kan aikin da aka dora masa.

Kazalika, ya nuna karfin gwuiwarsa a kan cewa kokarin da kwamitin ya ke yi, zai bawa Najeriya damar samun nasara a kan wannan annoba.

"A yau ne kwamitin ko ta kwana a kan shawo kan annobar cutar covid-19 ya kawo min ziyara domin yi min bayani a kan aiyukansu da halin da ake ciki.

"Ina mai farin ciki da godiya bisa jajircewarsu wajen sauke nauyin da aka dora musu. Ba ni da kokonto ko kadan a kan cewa kokarinsu zai bawa Najeriya damar samun nasara a kan annobar," a cewar Buhari.KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/


LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 






Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

Related Posts

0 Response to "Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 16, Jimilla 305"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?