--
Yanzu-yanzu: Sabbin Mutane 114 sun kamu da Coronavirus, 21 a Gombe

Yanzu-yanzu: Sabbin Mutane 114 sun kamu da Coronavirus, 21 a Gombe

Cibiyar hana yaduwar cututtuka a Najeriya watau NCDC ta sanar da samun karin mutane 114 da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya a ranar Juma'a, 24 ga Afrilu, 2020. Cibiyar ta bayyana hakan a shafin ra'ayinta na Tuwita inda tace: “An samu karin mutane dari da sha hudu(17) sun kamu da #COVID19"

80 a Lagos 21 a Gombe 5 a FCT 2 a Zamfara 2 a Edo 1 a Ogun 1 a Oyo 1 a Kaduna 1 a Sokoto A daidai karfe 11:30 na 24 ga Afrilu, an tabbatar kamuwar mutane 1095 da cutar COVID-19 a Najeriya An sallmi: 208 Mutuwa: 32


Kawo yanzu, ga jerin jihohin da cutar ta bulla da adadinsu: Lagos-657 FCT-138 Kano-73 Ogun-35 Gombe-30 Katsina-21 Osun-20 Edo-19 Oyo-18 Borno-12 Kwara-11 Akwa Ibom-11 Kaduna-10 Bauchi-8 Delta-6 Ekiti-4 Ondo-3 Rivers-3 Jigawa-2 Enugu-2 Niger-2 Abia-2 Zamfara-2 Sokoto-2 Benue-1 Anambra-1 Adamawa-1 Plateau-1

A bangare guda, Gwamnatin jihar Borno ta bukaci dakatar da wasu limamai uku na jihar a kan yin karantsaye ga dokar hana zirga-zirga ta jihar. Mataimakin gwamnan jihar, Umar Kadafur ne ya sanar da hakan yayin tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Maiduguri a ranar Juma'a. Kamar yadda jaridar Premium Times ta wallafa, sun tattauna ne yayin da yake duban yadda jama'a suke bin dokar hana zirga-zirgar da gwamnatin ta saka a jihar.


"Limaman da suka karya dokar sun hada da Goni Isa na Flatari ta Arewa, Goni Bashir na CMC da kuma Goni Gabchiya, babban limamin jami'ar Maiduguri. "Sun san da dokar hana zirga-zirgar amma sun ja sallar Juma'a, lamarin da ya taka umarnin gwamnatin jihar na kokarin hana yaduwar cutar Covid-19.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/


KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP

0 Response to "Yanzu-yanzu: Sabbin Mutane 114 sun kamu da Coronavirus, 21 a Gombe "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?