
Yanzu-yanzu: Mutane 86 suka kamu da Coronavirus ranar Lahadi, ta bulla a Borno da Jigawa (Kalli jerin)
Sunday, 19 April 2020
Comment
“An samu karin mutane tamanin da shida (86) sun kamu da #COVID19;
70 a Lagos
3 a Katsina
3 a Akwa Ibom
1 a Jigawa
1 a Bauchi
1 a Borno
Ga jimilla:
Lagos-
376 FCT-
88 Kano-
36 Osun-
20 Oyo-
16 Edo-
15 Ogun-
12 Kwara-
9 Katsina-
12 Bauchi-
7 Kaduna-
6 Akwa Ibom-
9 Delta-
4 Ekiti-
3 Ondo-
3 Enugu-
2 Rivers-
2 Niger-
2 Benue-
1 Anambra-
1 Borno-
2 Jigawa-
A baya, mun zakulo wasu nau'ikan abinci masu bunkasa garkuwar jiki, wanda babu shakka masu ta'ammali da su za su ci moriya wajen samun riga-kafin covid-19. A wannan lokaci da annobar covid-19 ta dugunzuma al'ummar duniya baki daya, baya ga kula da tsaftar jiki da muhalli, akwai kuma bukatar lura da irin abincin da ya kamata a ribata.
Ga jerin wasu nau'ikan abinci da na sha da suka kunshi sunadarai masu albarkar bunkasa garkuwar jiki kamar haka: Dangin kayan lemu:
(Lemun zaki, Lemun tsami, Lemun Taba, Tanjirin, Inibi) Dangin kayan lemu wanda a turance ake kira da Citrus Fruits, sun kunshi sunadarin Vitamin C, wanda yake taimaka wa jinin mutum bunkasa garkuwa ta yakar cututtuka.
1. Tattasai:
Jan tattasai ya kunshi sunadaran Vitamin C da kuma Betacarotene wadanda baya ga inganta lafiyar fata, suna kuma bunkasar garkuwar jikin dan Adam.
2. Tafarnuwa:
Bayan karin dandano ga abinci, tafarnuwa tana tasiri wajen bunkasa garkuwar jiki ta hanyar hana kamuwa da cutar hawan jini.
3. Citta:
Citta na da nasabar gaske wajen magance cututtukan da suka shafi mura, ta hanyar tsarkake kafofin shakar numfashi musamman makoshi. Tana kuma taimaka wa masu yawan tashin zuciya.
4. Alayyahu:
Tamkar Jan tattasai, alayyahu ya kunshi sunadaran vitamin C da kuma Betacarotene, masu taka rawar gani wajen bunkasa garkuwar jiki da zai yaki cututtuka.
5. Madarar shanu:
Vitamin D shi ne babban sunadarin da madarar shanu ta kunsa, wanda ya ke bajintar gaske ta hanyar bunkasa garkuwar jiki da kuma yakar cututtuka a jikin dan Adam.
6. Gwanda:
Gwanda ta kunshi sunadarai (Vitamin C, Folate, Potassium, B Vitamin) masu tabbatar da bunkasar lafiya a jikin dan Adam da kuma bai wa jiki garkuwa ta yakar cututtuka.
7. Naman Kaza:
Cin naman kaza bai takaita kadai a wurin motsa kunnuwa ba, domin kuwa har ta kashin kaza yana kunshe da sunadarai masu inganta lafiyar bil Adama.
8. Kifi mai ƙwanso:
Ire-iren namun ruwa wanda halittar su ta kasance a cikin ƙwanso kamar ƙaguwa da sauransu, su na da albarkar sunadarin zinc. Sunadarin Zinc yana bunkasa lafiya da kuma garkuwar jikin dan Adam.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP
0 Response to "Yanzu-yanzu: Mutane 86 suka kamu da Coronavirus ranar Lahadi, ta bulla a Borno da Jigawa (Kalli jerin) "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?