
Yanzu-yanzu: Majalisar wakilai ta yi wa SGF Boss Mustapha, ministan lafiya da shugaban NCDC kiran gaggawa
Tuesday, 28 April 2020
Comment
- 'Yan majalisar wakilan Najeriya sun yi wa sakataren gwamnatin tarayya, Mustapha Boss, ministan lafiya da shugaban NCDC kiran gaggawa
Majalisar wakilan ta yi hakan ne don su yi mata bayani a kan mace-macen da ke aukuwa a jihar Kano.
Mambobin majalisar dokokin tarayya sun dawo zaman majalisa bayan kimanin makonni biyar da tafiya hutu a kan annobar coronavirus. Yan majalisa na dattawa da na wakilai sun koma zauren majalisar a Abuja, a ranar Talata, 28 ga watan Afrilu, bayan sun tafi hutu duk a cikin matakan hana yaduwar cutar COVID-19 a kasar. A majalisar wakilan,
shugaban majalisa wakilan , Femi Gbajabiamila ya jagoranci mambobinta zuwa zauren, inda aka fara tattaunawa da misalin karfe 10:30 na safe, jim kadan bayan sun samu waje sun zazzauna. A yayin da ake tsaka da samun hauhawar masu COVID-19 a kasar, an bukaci 'yan majalisar su bayar da tazara a tsakaninsu ta hanyar tsallake kujeru bibbiyu wajen zamansu
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP
0 Response to "Yanzu-yanzu: Majalisar wakilai ta yi wa SGF Boss Mustapha, ministan lafiya da shugaban NCDC kiran gaggawa "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?