
Yanzu Yanzu: Karin mutane biyar sun kamu da coronavirus a Kano
Wednesday, 15 April 2020
Comment
- A yanzu jimlar mutane tara kenan suka kamu da annobar ta COVID-19 a jahar Rahotanni sun kawo cewa an sake samun karin mutane biyar da suka kamu da cutar coronavirus a jahar Kano. Ma’aikatar lafiya ta jahar Kano ce ta bayyana hakan a shafin twitter a ranar Laraba, 15 ga watan Afrilu. A sakon da ya wallafa a shafinta nata, ta ce ya zuwa karfe 10:25 na safiyar Laraba, adadin masu dauke da cutar a Kano ya kai tara.
Wednesday, 15th April 2020. As at 10:25 am, 5 additional cases of #COVID19 have been confirmed in @KanostateNg @NCDCgov @FMICNigeria @dawisu @NOA_Nigeria @Chikwe_I @NphcdaNG— Kano State Ministry of Health (@KNSMOH) April 15, 2020
#StaySafeNigeria #StayHome pic.twitter.com/8KfIOT2Bih
A baya mun ji cewa mai girma gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bada umarnin rufe jihar na mako daya.
Dokar hana shige da fice a jihar Kano din za ta fara aiki ne daga ranar Alhamis, 16 ga watan Afirilun 2020. Kamar yadda mai bada shawara ta musamman ga gwamnan ya wallafa, ana sa ran dokar hana shige da ficen za ta yi aiki ne mako daya cif kafin a ga abinda hali yayi.
A wani labari na daban, Legit.ng ta wallafa cewa gwamnatin jihar Kano, karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Ganduje ta ce za ta rufe wasu daga cikin kasuwannin da ke jihar tare da tsananta dokar hana shiga da fice a kan iyakokinta. Hakan kuwa ya faru ne sakamakon bullar muguwar cutar coronavirus a jihar a ranar Asabar. Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya shaidawa BBC cewa tuni aka killace wanda aka samu da cutar a asibitin Pfizer na kwanar Dawaki.
KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇
LATSA NAN DOMMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE
KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Yanzu Yanzu: Karin mutane biyar sun kamu da coronavirus a Kano "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?